Connect with us

SIYASA

Kujerar Sanatan Katsina Da Funtua: Mandiya Da Barkiya Na saman Igiyar Ruwa – Jigon Jam’iyyar APC

Published

on

Wani jigo a jam’iyyar APC a jahar Katsina ya yi hasashen idan ba a dauki matakin gaggawa ba jam’iyya APC na iya rasa kujerar Sanata a Katsina ta tsakiya da kuma yankin Funtua saboda irin kalubalan da ya hango.
Sakataran Kungiyar APC soshiyar Midiya na Yankin arewa masu yamma, Alhaji Dahiru Mani ya yi wannan hasashe a lokacin da ya ke zantawa da wakilin LEADERSHIP A Yau a Katsina dangane da zaban da ke tafe wanda ya ce babu inda ake hangen matsla kamar wuraran nan guda biyu wato yankin Katsina da kuma Funtua
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina Alhaji Bello Mandiya shi ne dan takarar jam’iyyar APC mai neman Sanatan shiyyar Funtua sai kuma tsohon shugan hukumar kula da gyaran hanya ta kasa FERMa Injiniya Kabir Barkiya na neman Sanata a yankin Katsina ta tsakiya
Ya kara da cewa yankin Daura ka dai ya zuwa yanzu babu wata matsala, amma dai sauran wurara ya kamata a dubu tun da safe, ya ce duk da dai ba za su iya hana cin zabe ba, amma akwai bukatar a duba lamarin, inda ya ce akwai al’umma da dama musamman a shiyar Katsina da Funtua da suka sha alwashin cin amanar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Alhaji Dahiru Mani ya kuma bayyana cewa mutanen sun kafe ne akan wasu dalilin wadanda a gwamnatance ko a jam’iyyance ba su da wahalar magancewa ma damar za a zauna da su da al’immar yankunan su domin jin korafinsu da kuma neman goyan bayansu akan wannan tafiya ta APC
Daga cikin irin abubuwan da ya hango sun hada da koken da wasu ke yi na cewa Dan takarar bai je neman gudnmawarsu ba, su kuma ba za su yi mubayi’a ba, wasu na koken ba a neme su cikin hidimar ba.
Kazalika ya kara da cewa akwai masu ra’ayin babu ruwansu, akwai masu cewa an bar su baya har yanzu, wasu kuma suna koken cewa suna marawa dan takara baya amma ya fadi wasu na koken ‘yan siyasar yankin da wadanda aka baiwa mukamai ba su daratta su
Ya ce wasu na koken masu mukaman yankinsu ba su taimakon al’ummar yankin su , ya ce idan aka yi nazari za a fahimci cewa duk wani mai korafin baya korafi da gwamna Masari ko kuma gwamnatinsa bata yi masu komi ba.
A karshe ya nuna bukatar da ke akwai na ganin an zauna da wadannan al’ummomin shiyoyin nan guda biyu, domin samun nasara cin zaben jam’iyar APC a zabe mai zuwa na 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!