Connect with us

SIYASA

Kungiyar Amana/Ijaba Ta Shirya Taro Kan Zabar Shugabanni Nagari A Bauchi

Published

on

Wata kungiya mai zaman kanta mau suna AMANA/IJABA FOUNDATION, ta gudanar da taron kara wa juna sani na wuni daya a Bauchi, mai taken ‘Muhimmancin zaben shugabanni na gari a mahangar addini’.
Taron, ya gudana ne a babban dakin taro na Stable Plaza da ke garin Bauchi, wanda ya samu mahalarta daga ko’ina a fadin kananan hukumomin jihar Bauchi 20, tare da samun wakilai daga dukkan kugiyoyin addinin musulunci da ke jihar ta Bauchi.
Da yake gabatar da jawabin maraba a yayin taron, shugaban kungiyar Malam Mustapha Baba Ilelah, ya bayyana cewa, wannan kungiya an kafa ta ne tun shekarar 2007, da zummar zamowa kafar wayar da kan al’ummar musulmi akan dukkan wani janibin da ya shafi rayuwar dan Adam.
Malam Mustapha Baba Ilelah, ya nuna farin cikinsa bisa yadda al’umma suka amsa gaiyatar kungiyar, daga dukkan wani sako da lungu na dukkan kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi, wanda ya ce hakan ya nuna cewa abin da aka sanar a wajen taron zai yi tasiri a zukatan al’umma, “don kuwa dimbin wakilan jama’a da suka halarci taron nan, za su isar da abin da aka sanar da su wa al’umominsu idan sun koma garuruwansu,” Inji shi
Shugaban taron, ya mika godiyarsu wa Malaman da suka gabatar da kasidu da mukalu a yayin taron, sannan yayi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da abin da suka koya, da nufin ganin cewa an zabi shugabanni nagari a yayin babban zabe mai zuwa a shekarar 2019, don ganin al’umma ta samu shugabanni nagari da za su kawo canje-canje masu ma’ana da za su bunkasa jin dadi da walwalar al’ummar jihar Bauchi da ma kasa baki daya.
Sanannun Malamai biyu ne suka gabatar da kasidun da suka shafi tasari da alfanun da shugabanni nagari suke da shi wa rayuwar al’umma, wadanda suka yi dogon bayanai tare da kawo hujjoji a nassin Alkur’ani mai girma da kuma Hadisan Manzon Allah Annabi Muhammadu (S.A.W).
Malami na farko da ya fara gabatar da kasida a wurin taron shi ne Dakta Muhammad Mujtaba Abdulkadir, Malami a kwalejin nazarin Shari’ar musulunci da ke garin Misau a jihar Bauchi, wanda ya gabatar da mukalarsa mai taken ‘TSARIN SHUGABANCI NAGARI GA AL’UMMAH’.
Dk. Mujtaba Abdulkadir, ya bayyana wasu abubuwa guda biyar da ake son kiyayewa ta hanyar ganin an samu shugaba nagari, wanda a kalmar Larabci ake cewa (Al Darurat al Khamas), su ne hankali, addini, dukiya, rai da kuma tsatso.
Har-ila-yau, cikin mukalar da Dakta Mujtaba ya gabatar, ya bayyana siffofin shugaba nagari guda biyu, wadanda suka hada siffofin cancanta da na kamala, wadanda suka kunshi na bangaren addini da kuma na zamantakewar al’umma.
Malamin, ya kara da cewa, shugaba nagari shi ne wanda ya siffantu da dabi’oin nagarta da ake siffanta shugaban halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) da su, wadanda suka hada da Ilimi, hakuri, nagarta, juriya, kawaici, tausasawa, tausayawa, shimfidar fuska, sadaukar da kai don al’umma, da sauran dukkan wasu dabi’u nagari, da kuma guje wa dukkan siffofi wadanda suke kishiyoyi ne ga ga halayen kirki da nagarta.
Ya kara da cewa, a mahangar; addini ana bukatar shugaba ya zamo dan kasa nagari wanda yake cikin al’umma, sannan ya zamo Da ne shi ba Bawa ba, ya zamo mai hankali ba yaro ba, ya zamo yana da hankali ba mahaukaci ba, ya zamo na miji ba mace ba, ya zamo adali ne shi, don shugabancin fasiki ko azzalumi bai halatta ba a musulunci, don kuwa dukkan nau’in fasikanci da zalunci cin hanci ne da rashawa.
Dk. Mujtaba, ya ce ana bukatar shugaba ya zamo mutum ne mai nuna ba sani ba sabo wajen yin hukunci na adalci a tsakanin mabiyansa, sannan musulunci yana da bukatar shugaba ya kasance mutum ne mai lafiya, wanda baya da wasu cututtuka da suka hada da gurgunta, makanta, hauka da sauransu, kuma ya zamo shi kwararre ne wato masanin dabarbarun rayuwa da kuma kare rayuwar a dukkan matakai ko mafi yawan bangarorin rayuwar al’umma.
Ya daura da cewa, ana son shugaba ya zamanto mutum ne wanda baya da nuna tausayi a wajen tsaida haddi, hukunci da kuma jajircewa wajen ganin an maido da hakkoki ga masu shi.
Da yake gabatar da tasa mukalar, Babban Limamin Masallacin Jumu’a na Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi (ATBUTH) Imam Aminu Aliyu Ahmad, ya gabatar da kasidarsa ce mai taken “GUDUMAWAR AL’UMMAH DON ZABEN SHUGABANNI NAGARI” inda ya bayyana wajibcin da ke kan al’umma wajen zaben shugaba nagari, yana mai bayyana cewar ta fuskacin zabin shugaba na gari ne kowace al’umma ta samu ginuwa.
Imam Aminu Aliyu Ahmad, ya kawo Hadisin da Annabi Muhammadu (S.A.W) ya ke cewa, duk wanda ya mutu ba wani shugaban da ya zaba wa kansa, to, ya yi mutuwa ta jahilai.
Ya kara da cewa, daga cikin mutane akwai wadanda nasiha, jan hankali, rarrashi da lallabi ba su musu amfani don su gyaru su su sa su bi doka da oda, sai shugaba ya hada da amfani da karfi.
Malamin, ya yi kira ga al’umma da su zabi shugaba bisa cancantarsa da kuma kyakkyawar tunani da suke masa, na cewa zai iya amfanar da rayuwar al’umma, ba wai mutum ya zabi shugaba don yana ganin cewa idan ya hau karagar mulki zai taimake shi shi kadai ba.
Ya ce dole ne masu zabe su duba wanda ya cancanta da dacewa akan kujerar da za su zabe shi, don shugabanci yana da rukunai guda biyu, iyawa da kuma amana, don haka ya ce tilas ne akan al’ummah da su zabi wanda suke ganin ya cancanta da kujerar da yake nema, ba wai kawai a duba shi ta fuskar cewa idan wane ya hau mu namu ya samu ba.
Cikin wadanda suka yi tsokaci a wajen taron sun hada da Farfesa Bala Suleman Dalhat, Malami a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, da Malam Dan’azumi Musa Tafawa Balewa, wadanda suka yi jan hankali wa al’umma wajen ganin an zabi shugabanni nagari, wadanda ake da kyakkyawar zabo a kan su.
Su ma ‘yan siyasa sun samu wakilci a taron, don kuwa akwai fitattun ‘yan siyasa a jihar Bauchi da suka halartar kamar Alh. Danladi Danbaba (Maza Wajen Bauchi/Sarkin Fadan Miri), Hon. Hamza Maikudi Gawo, Alh. Muhammadu Abubakar Sade (Usama) da sauransu, inda suka nuna farin cikinsu tare da yin kira ga kungiyar AMANA/IJABA FOUNDATION, da ta kara fadada irin wannan taro ya zuwa matakin kasa baki daya, don a cewarsu, al’umma suna da bukatar samun shugabanni nagari wadanda za su kyautata rayuwarsu.
Sun bayyana cewa wannan taron ya zo a daidai lokacin da ya dace, ganin cewa ana daf da lokacin da za a sake gudanar da babban zabe a kasar nan baki daya, don haka suka bukaci mahalarta taron da su wayar da kan al’umominsu yayin da suka koma garuruwansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!