Connect with us

LABARAI

Kungiyar Masu Sauke Kayan Gwari Ta Yi Taron Hadin Kai A Kano

Published

on

Kungiyar cibiyar kasuwar hada hadar sauke kayan gwari da sayarwa ta Nijeriya mai helkwata a jihar Legas ta gudanar da taron ta na shuwagabannin kungiyar domin tabbatar da hadin kai ‘yan kasuwar a garin Kano taron wanda ya gudana a gidan tsohon shugaban kasuwar Alh Isah Mohamed mai shinkafa dake Kano a cikin makwanni biyu da suka wuce taken wannan taron dai shine “neman karin hadin kai da zaman lafiya a unguwar mile 12 da jihar Legas baki daya” taron ya gudana jim kadan bayan da aka daura aure a gidajen wandansu daga cikin manyan kasuwar guda biyu Alh Mohmadu Abdu Kudan Hunkuyi wanda shi ne babban sakataren kasuwar da Alhaji Abdu kura shi ma shi ne sakataren bangaren ‘yan Albasa
A jawabinsa a wajen taron shugaban kasuwar mile 12 Alhaji Haruna Mohmed Tamarke mai Dankalin Turawa ya ci gaba da cewa wajibi ne a garesu su kara kaimi a wajen hada kan yan kasuwar da dorasu a kan lafiya mai dorewa a kowane lokaci sannan shugaban ya umurci al’ummar kasuwar su ci gaba da hada kawunansu da bin dokokin kasuwa domin kara dankon zumunci a tsakaninsu sannan ya ci gaba da cewar wajibi ne shuwagabannin kasuwar musamman na bangaren daban daban na kasuwar da su ci gaba da gudanar da aiyykan alheri domin mabiyansu su dauki darasi a wajen kare mutuncin kasuwar da sauran makamantansu.
A nasa jawabin, tsohon shugaban kungiyar yan kasuwar gwarin Alhaji Isah Mohmed mai shinkafa ya yi kira ga yan kasuwar ne da su kara kaimi a wajen ayyukan da zasu wanzar da zaman lafiya a unguwar mile 12 da jihar Legas gaba daya sannan ya kara ummurtar yan kasuwar da su ci gaba da tsaftace kasuwancinsu a lokacin da suke cikin kasuwanci domin samun halartacciyar riba a duniya da kuma lahira sannan yakar da yabama shugaban nin kasuwar a karkashin jagorancin shugaban kasuwar Alh Haruna mohmed Tamarke a wajen hada kan jama’a da kare mutuncin Kasuwar.
A jawabinsa na nuna farinciki gameda wannan taro na hadin kai da neman Karin samun zaman lafiya ga al-umar kasuwar mile 12 da jihar Legas bakidaya Alh Muhmadu Abdu kudan wanda shine Babban sakataren kasuwar ya nuna farin cikinsa ne gameda yanda al-umar kasuwar suka hada kansu wajan basu kyakkyawan hadin kai a kowane lokacin abisa aikin kasuwar injishi da fatan Alheri Amin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!