Connect with us

LABARAI

Likitocin Sun Nemi A Kawo Karshen Garkuwa Da Mutane A Jihar Ondo

Published

on

A ranar Litinin ne Likitoci daga jihar Ondo sun nemi a kawo karshen garkuwa da mutane a duk fadin jihar, inda suka baiwa gwamnan jihar Rotimi Akeredolu kwanaki bakai a kan ya kawo karshan wannan matsala. Likitocin sun yi wannan kira ne amadadin kungiyar likitoci ta kasa reshan jihar Ondo, sakamakon yin garkuwa da ‘yan bindiga suka yi da likitocin guda uku na asibitin tarayya da ke Owo cikin makon da ta gabata. Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da likitoci mata guda biyu da kuma namiji daya. An yi garkuwa da sune tare da malaman kwalejin kimaya na Rufus guda biyu a kauyen Amurin kan babban titin Akure zuwa Owo da ke cikin karamar hukumar Owo ta jihar. An bayyana cewa, an saki wadanda aka yi garkuwa da su.
Da yake ganawa da manema labara a Akure, shugaban kungiyan likitocin Dakta Wale Oke ya bayyana cewa, mambobinsa suna aiki ne cikin fargaba. Oke ya kara da cewa, kungiyar ba za ta samu kunciyar hankalin gudanar da aiki yadda ya kamata ba, inda dai har gwamna ya kasa kawo karshan yin garkuwa da mutane a cikin jihar. Ya ci gaba da cewa, “A cikin wata uku, an samu lamarin garkuwa da mutane har guda uku wadanda suka hada da likitoci, ma’aikatan lafiya da kuma sauran mutane a cikin wannan jiha. Lamarin yana kara karuwa sannan ba za mu amince ba ‘ya’yan kungiyarmu suna gudanar da aiki ciki fargaba, inda suke zuwa wajen aiki ya zama wani tashin hankali. “Muna kara jadada wa gwamnati bukatar mu na kawo karshan barazanar da ‘ya’yan kungiyarmu suke fuskanta a cikin wannan jihar. “Har ila yau, muna bukatar kawo karshan wannan lamari a ciki kwanaki bakwai.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!