Connect with us

KIWON LAFIYA

Maganin Matsalar Rashin Ingantaccen Abinci Zai Taimaka Wajen Kawar Da Fatara A Nijeriya – Masani

Published

on

Kamar kashi 33 na al’ummar Nijeriya zasu iya fita daga cikin matsalar fatara, wannan kuma zai iya faruwa ne idan har kasar zata dauki wani babban mataki dangane da rashin samar da ingantaccen abinci mai gina jikin kananan yara,. kamar dai yadda wani kwararre a ala’amarin daya shafi kayayyakin abinci Bamidele Omotola ya bayyana. Bugu da kari shi al’amarin yakki da rashin ingantaccen abinci zai taimaka ma kasa ta bangaren tattalin arziki.
Mista Omotola ya yi wannan jawabin ne lokacin taron manema labarai akan rashin ingantaccen abinci na kananan yara a Yola babban birnin jihar Adamawa, ranar Laraba inda yace yaron da yake fuskantar matsalar rashin ingantaccen abinci mai gina jiki, bai da wani abinda zai bayar da gudunmwa wajen ci gaban tattalin arzikin kasa.
Shi taron na manema labarai asusun gaggawa ne al’amarin daya shafi kananan yara na majalisar dinkin duniya ya shirya shi, wanda kuma, sashen kula da ci gaban kasa da kasa, yana da taken t ( “ Sa jari al’amarin rashin ingantaccen abincin gina jiki na kananan yara, kamar wani al’amari wanda ake yi saboda gaba”
Rashin ingantaccen abinci yana faruwa ne lokacin da mutane suka dauki wani lokaci wanda basu cin abinda ya kamata, ko shan abinda ya dace, abinda ya kamata, da kuma irin nau’oin abincin daya dace a ci, sai kuma irin kayayyakin abincin da kuma abubuwan da suka kunsa. A duniya kusan shi al’amarin yana taimakawa wajen samun rabin mutuwar kananan yara, wannan ya nuna ke nan fiyea da yara milyan uku ko wacce shekara.
Mista Omotola ya bayyana cewar shi yaki da rashin ingantaccen abinci wani abu ne wanda ya dace ayi shi a Nijeriya, saboda ko wanne tattalin arzikin daya ke kashi 50 nayara suna da matsala wani abin ban takaici .
“ Idan har kasar Nijeriya ta samu fita daga cikin matsalar rashin ingantaccen abinci mai gina jiki wanda musamman kananan yara ne suke amfani da shi, kashi 33 na al’ummarta zasu samu fita daga cikin kuncin fatara, su kuma taimaka ma ‘ya’yansu yadda zasu samu kyakkyawar rayuwa ta gari.” kamar dai yadda Mista Omotolan ya bayyana .
Yakra jaddada cewar sa jari akan al’amarin daya shafi rashin ingantaccen abinci mai gina jiki, na kananan yara, wannan wata babbar dam ace, ta samun canji wanda ya kunshi zamantakewa da kuma karuwar tattalin arzikia nahiyar Afirka.
“ Ga ko wacce dala daya wadda aka zuba jari wajen rage matsalar rashin ingantaccen abinci mai gina jikin kananan yara a nahiyar Afirka, za a ribar dala goma sha shida , sai kuma yadda har za a samu damar mnaganin mutuwar kusan rabin yara wadanda suke mutuwa asanadiyar haka. ga kuma wata gara basa ta karuwar yara wadanda suka isa shiga makaranta da koda shekara daya.”
Mr Omotola noted Ya yi kira da a kara zuba jari saboda a tabbatar da samar da isasshen abinci, saboda akawo karshen yunwa nan da shekara ta 2030 wanda wannan muradi ne na biyu na daga cikin muradan ci gaba na majalisar dinkin duniya (SDGs).
t Duk da yake shi al’amarin rashin ingantaccen abinci mai gina jikin kananan yara da sauran mutane, abin yafi kamari ne a sashen Arewa maso gabas, koda yake dai akwai wasu wurare cikin jihohi a fadin tarayyar Nijeriya inda ake samun irin wadannan matsaloli na rashin ingantaccen abinci ma gina jiki a Nijeriya.
Hakanan ma daga cikin yara shida a cikin jihohi uku wadanda ala’amarin ta’addanci na kungiyar Boko Haram ya sha, suna fama da tsananain rashin ingataccen abinci mai gina jikiHe sa
Wadannan jihohi sun hada da Adamawa da Yobe da kuma Borno.
Shima a nashi jawabin Ministan watsa labarai da al’adu Lai Mohammed ya bayyana cewar daukar mataki wanda za ayi maganin rashin ingantaccen abinci mai gina jiki, wata hanya ce wadda za a iya cimma muradan ci gaba.
Shi dai Ministan shugaban cibiyar kula da harkokin yara ta ma’aikatar labarai Olumide Osanyinpeju, ya yi kira da a kara zuba jari ta banagren samar da ingantaccen abinci mai gina jiki, saboda hakan zai taimaka wajen yadda rashin shi yake.
Shi ma jami’in al’amarin daya shafi abinci na ofishin majalisar dinkin duniya ofishin jihar Bauchi Martin Jackson ya yi karin haske akan matakan da aka dauka, tare da taimakon Hukumar ci gaba ta kasa da kasa, saboda a samu canza yadda al’amuran suke a sashen Arewa maso gabas.
Ya bayyana cewar ya ji dadi matuka akan tsare -tsaren majalisar dinkin duniya take yi, wadanda ya ce,sun yi matukar taimakawa wajen canjin da aka samu a shi sashen na Arewa maso gabas.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!