Connect with us

KASUWANCI

Masu Depo-depo Na Man Fetur Sun Dakatar Da Ayyukansu

Published

on

A ranar Lahadi ne 9 ga watan Disambar 2018 ne masu defo-defo da kuma kungiyar masu sayar man fetur ta kasa ta umarci yayan su dakatar da ayyukan su har sai gwamnatin tarayya ta biya bashin da masu sayar da man na rarar kudin mai da suke binta. Kunguyar ta DAPPMAN, ta fitar da sanarwar ta awa 24 bayan da gwamnatin tarayyar ta sanar cewar zata biya bashin na naira biliyan 236 ga dukkan masu sayar da man a ranar juma’ar data wuce na biyan bashin na farko na rarar man da suke bin gwamnatin. Da yake mayar da martani a kan cewar ko kungiyar zata shiga yajin aijin da ta yi niyyar shiga sabida kin amincewar da gwamnatin ta yi da fako na biyan bashin, Babban Sakataren kungiyar ta DAPPMAN, Olufemi Adewole ya ce, kwarai zamu shiga yajin aikin tunda har yanzu bamu samu tabbaci ko gwamnatin zata buya bashin ba don mu samu mu biya albashin watan Disamba. Olufemi Adewole ya ci gaba da cewa, kungiyar ta dauki manyan matakai don ganin ta dakatar da wahalhakyn da ya yan ta suke fuskanta sakamakon sallamar su daga aiki bayan shekaru uku data shafe ta na tattaunawa da gwamnatin akan kokarin kungiyar na son gwamnatin ta biya ta bashun nata.Ya kara da cewa,har zywa yau, tattaunawar da gwamnatun bata biya judin sabulu ba. Acewar Adewole, kamar yadda juka sani ne kungiyar ta sake yin nazari a kan dakatarwar da ta yiwa yayan kungiyar bayan wa’adin da ta baiwa gwamnatin a ranar 25 ga watan Disambar 2017, wanda ta janye bayan da muhimman mutane a kasar nan suka shiga cikin maganar, inda gwamnatin ta yi alkawarin biyan bashin a kan lokaci. Sai dai ya nuna takaicin a kan cewar har zuwa yau, kimanin shekara daya kenan babu wani abu da muka samu sai dai gayyatar tattaunawa wadda kuma bata daktar da gabatar da bukatun mu na yau da kullum ba na wannan bashin da bakuna da hukumomi muma suke bin mu.
Adewole ya sanar da cewa, kungiyar ta DAPPMA ta sanar da gwamnatin a hukumance ta hanyar ma’aikatar kudi da kuma ofishin dake kula da basusuka na kasa, inda ofishin kai tsaye ya sanar da fadar Shugaban kasa. Ya ce, kungiyar ta sanar da gwamnatin a kan kalubale da take fuskanta na rashin kudin biyan albashin ma’aikatan ta sama da ranar 30 ga watan Nuwambar 2018 wanda zatk iya biyan su ne kawai in an biya ta bashin na rarar mai da kuma kudin musaya na kasar waje bayan data gabatarwa da gwamnatin takarda a ranar 31 ga watan Disambar 2018. Ya sanar da cewa, ci gaba da tattaunawar da gwamnatin, hakan ya nuna alamun waiwayowar gwamnatin a kan bashin sai dai har yanzu ba’a samu tabbacin ko gwamnatin zata biya bashin gaba daya ba. Acewar sa, tunda mun sallami ma’aikatan namu, baza a iya gudanar da duk wani aiki ba, har sai gwamnatin ta biya mu bashin namu da muke binta na rarar man da kuma biyan kudin ruwa na ranar 31 ga watan Dismbar 2018. A karshe Adewole ya ce,wannan matakin ya zama dole a kan ko wanne dan kungiyar na dole ne subi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!