Connect with us

LABARAI

Masu Kasuwannin Waya Sun Yaba Da Kulawar Da Gwamna Ganduje Ya Ba Su

Published

on

Kungiyar masu kasuwannin saida waya na jihar Kano sun bayyana cewa jin dadinsu da kulawa da Gwamnatin Kano take ba su da har ta debi dinbin masu harkar gyaran wayar hannu da ba su horo da tallafi. Shugaban Kungiyar yan kasuwar waya ta Bata Global, kuma mataimakin Shugaban hadakar kungiyoyin kasuwanin saida waya na jihar Kano. Alhaji Tijjani Isma’il Ahmad ya bayyana haka.
Ya ce, a kalla lokaci guda Gwamnati ta debi masu gyaran waya kusan 4,000 aka basu horo na kwanaki hudu aka kuma basu kayan gyara na kimanin kudi N36,000 wannan abu ya yi musu dadi kuma za su ci gaba da bai wa Gwamna Ganduje hadinkai da goyon baya don kai wa ga nasara a zabe mai zuwa.
Alhaji Tijjani ya ce, wannan horo da tallafi da aka yi musu ya dada habaka harkar da dama tana kauda zaman banza a tsakanin matasa, horon ya kara samar da wasu a cikin harkar sakamakon wannan kyakkyawan tunani na Gwamna Ganduje, suna fata Gwamnatin za ta kara maimaita musu irin wannan ba da horo da tallafi da anfanar wasu da dama daga ciki da basu samu ba.
Alhaji Tijjani Isma’il ya ce, yanzu haka a ciki da sakon Kano a kasuwanni da wurare daban-daban suna da mambobi da suka kai guda miliyan daya da suke da rijista da su kuma suna da kyakkyawar alaka da hukumomin tsaro da suke basu shawara ta yanda za su tafiyar da harkokinsu da kaucewa abin da bai kamata ba. Suna kuma wayar da kan mambobinsu a kan tsare gaskiya da amana da gujewa sayen kaya na rashin gaskiya duk abinda za su saya su tabbatar da sahihancin mai shi sannan su saya ta hanyar ya ba su kwalin waya da rasit na ainihin saye da shaida.
Ya ce, matsalar da tafi damunsu shi ne na kawo wayoyin da ba su da kayan gyara kuma ba su da rijista da hukumar sadarwa ta kasa, amma sun sami zama da hukumar ta NCC ta ce, za ta ba su sunayen wayoyi da ba ta amince da su ba don su daina sayensu,
Alhaji Tijjani Isma’il Ahmad ya ce, suna mutukar murna da farin ciki da matakin da Gwamnati ta yi musu na cewa za ta gina babbar kasuwa ta hada-hadar wayoyi a jihar Kano hakan zai rage musu matsaloli da suke fuskanta duba da cewa a cikin kasuwannin wayoyi dake Kano guda biyu ne kawai Gwamnati ta gina sauran duk haya suke karba da suke fuskantar barazana iri-iri na karin kudin haya da kuma tashinsu ba za ta ba tsammani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!