Connect with us

LABARAI

Matsalar Tsaro Tsakanin Najeriya da Nijar: Za Mu Ci Gaba Da Mutunta Yarjejeniyar Da Muka Kulla –Gwamna Masari

Published

on

Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya nanata kudirin gwanatinsa na ci gaba da mutunta yarjejeniyar da aka kulla tsakanin jihar Katsina da kuma jamhuriyar Nijar akan matsalar tsaro.
Gwamna Masari yana magana ne a lokacin sa hannu akan yarjejeniyar da akulla a shekarar da ta gabata wanda yanzu aka kaddamar da ita a hukumance a filin wasan kwallon dawaki na Katsina
Alhaji Aminu Bello Masari wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Mannir Yakubu ya ce an kulla wannan yarjejeniya ce domin a samu sakamako mai kyau game da matsalar rashin tsaro da aka fuskanta a lokutan baya, wanda yanzu ake son a yi maganin matsalar baki daya tare da farfado da tattalin arziki da kuma daidaita tsakanin makiyaya da fulani
Ya kuma yaba da kokarin kwamitin da aka dorawa alhakin yin wannan aikin da ake kira da kwamitin jahohi masu makwabtaka da juna domin dai su magance wannan matsala ta tsaro
Tunda farko da yake nasa jawabi sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana cewa wannan yarjejeniya da aka kulla ta haifar da da mai ido.
A cewarsa yanzu makiyya suna barin manoma su kauda amfanin gonarsu kafin su kora dabbobinsu cikin gonakan, abinda ba saba gani ba a shekarun da suka gabata.
Shima a nasa jawabin gwamnan jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar, Injiniya Zakari Ummaru ya nuna matukar godiyarsa ga gwamna Masari akan kulla wannan yarjejeniya tsakanin jihar Katsina da kuma jamhuriyar Nijar musmaman jihar Maradi
Ya ce sakamakon samun nasarar da wannan yarjejeniya da aka kulla yanzu haka jahohi irin su Sakwato da Kebbi da kuma Jigawa sun dukufa wajan ganin sun kulla irin wannan yarjejeniya da jamhuriyar Nijar ta bangarro da suke da iyaka da su da suka hada jihar Dosa da Tawa da kuma Zinder
A karshen taro an gudanar da wassanin gargajiya wanda yake nuni da kara kulla zumunta da ‘yan uwantaka da suka da wasan Dambe da Sharo da Rawar Rakumma da Kokawa da sauransu. Haka kuma Gwamna Masari ya mika kyautar Mota kiran Hiliud ga wannan kwamitin domin ci gaba da ayyukansa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!