Connect with us

DAGA NA GABA

Me Ya Haddasa Bara Da Cirani A Arewa?

Published

on

Dabi’ar cirani da barace-barace da bangar siyasa da jahilici da Talauci kusan su ne abubuwan da ake wa kallon sun yi kaka-gida a Arewacin Nijeriya. Kullum matasan arewa musamman wadannda suka fito daga karkara ba su da wani gurin da ya wuce su tafi kudancin kasar nan cirani, ko neman kudi. A arewa ne mata ke hayar kananan yara su na tafiya da su kudancin kasar nan domin yin barace-barace. Alkalumma sun tabbatar da cewa duk in da ka ga mata na bara ko tsayawa bi sa Shataletale a kudancin kasar nan domin neman taimako, ko bara to ba bu ko shakka daga arewa suka fito.
Duk wasu sana’o’in kaskanta ko ci baya da ake yi a kudancin kasar nan ‘yan arewa ne ke gudanar da su. Da yawan matasa da matan da ba su zuwa makaranta a kasar nan daga arewa su ke. Duk wannan tabarbarewa me ya kawo ta? Arewa ta rasa abubuwa da yawa, shugabannin da suka shude da yawa ‘yan arewa ne amma me suka tsinanawa arewar?
Wani abu da zai daure maka kai shi ne ko da Turawan mulkin mallaka suka zo arewa sun tarar da ita da cigabanta da bunkasuwarta da siturarta da muhallinta da tsarin shugabancin ta da iliminta da kome nata sabanin kudu da suka tarar hargitse sai da su ka yi kokarin gyara ta, amma me ya sa komi a kasar nan lalattace sai dai ace Arewa? Shin wadanda suka gina Arewa a farko irin Su Sardauna da ire-irensa sun yiwa Arewa abin da ya kamata kuwa? In sun yi mata me ya sa Arewa ta zama haka? Shin Arewa Alfarma da ke bukata kamar yadda aka yi ta a baya, Ko baka cancanta ba in dai kai dan arewa ne sai a baka dama? Ina ganin wannan alfarmar da magabatan Arewa suka yi a baya shi ne ginshikin kasha Arewa, kuma shi ne ya sanya Arewa shiga halin da take yanzu.
Zamu dauki abubuwan nan daya bayan daya mu kalle su, wata kila zamu gano me Arewa ke bukata domin ta wanzu cikin Nasara.
Za mu fara da cirani da barace-barace, me ya sa matasan Arewa ke tafiya cirani a kudancin kasar nan? Amsoshin suna da yawa, wata kila wani ya ce, Talauci, wani kuma ya ce yawa da mutanen Arewa suka yi, dole sai sun bar arewar in su na so su wala, wani kuma na iya ce ma Jahilci. Ni a wuri na amsar ba wata wahala gareta ba, domin zaka yi abun nan da ake cewa halin Bahaushe wato tambaya cikin tambaya, shin me yasa ‘yan kudancin kasar nan ba sa zuwa Arewa cirani da barace-barace? Wata kila, kace ai yan kudu sun cika arewa gasu nan a Kano da Katsina da sauran Jihohin Arewa, ace kuma ba su zuwa cirani? To kwantar da hankalinka ka tsayan ka natsu ka diba kaga su ciranin da suke zuwa irin namu ne? ka taba ganin wani dan kudancin kasar nan a arewa ya na maka Shu-shana, ko gyaran akaifa, ko tura baro, ko dako ko matan su na barace-barace a titina da sauran kananan Sana’o’in da mu ‘yan arewa muke yi a cen? Ko ba komi su suna da abin da ake cewa “Hannu da yawa maganin kazamar miya” domin masu hali a cikin su suna taimakawa ‘yan uwansu, su saka su cikin sana’o’insu kuma su sanya hakuri har su koya. Wannan ne ya tuna man da wani labari da wani Marubuci ya kawo a cikin littafinsa mai suna “Yunkurinka Makomarka” a cikin ya ba da labari wani malami da ya ke son isar da wani sako ga dalibansa, sai ya tattara su sannan ya ba kowa mabusa ya ce ya rubuta sunansa cikin mabusar, sannan ya hura ta ya daure, kowa ya yi haka sannan ya nuna masu wani daki ya ce kowa ya kai tashi ya jefa.
Bayan da suka gama jefa mabusar a dakin sai ya ce, ya basu minti biyar kowa ya je ya dauko ta shi, haka sukaje sukai ta turoroniya, domin kowa ya dauko ta shi, amma har wa’adin mintunan suka cika, daga karshe suka fito ba wanda ya dauko ta shi. Sai ya ce masu to ya kara basu wani minti biyar din su koma, amma yanzu duk wanda ya ga ta wani ya miko mashi, har ya kai ga ganin tashi. Da suka koma sai gashi kasa da minti uku kowa ya fito rike da mabuasar sa.
Darasin da wannan labari ke dauke da shi a nan shi ne, taimakekeniya, in ka taimaki dan uwanka kaima sai ka samu abin da ka ke bukata cikin nasara, domin lokacin da zaka ga mabusar wani ka miko mashi kaima lokacin za a ga taka a miko maka. Wannan shi ne abinda muka rasa a Arewa, bamu taimakon junan mu, mutum na da halin da zai taimaki dan uwansa ko mutanen unguwarsu amma abun ya gagara sai dai ganin kyashi, da jin zafi da kuma kushe da hassada. Me zai sa mutanen Arewa ba za su yi koyi da abin da ya faru a cikin labarin nan ba su rika taimakaon ‘yan uwansu? Sau da yawa mutum na da abun da zai taimaki ‘yan uwansa amma sai ya kyale su, ina ganin wannan na daga cikin dalilan da ke haddasa tafiya barace-barace da kuma cirani a kudancin kasar nan saboda rashin taimakekeniya. Domin kowa ya sani a kudancin kasar nan suna taimakawa ‘yanuwansu musamman ta bangaren karatu, wanda a nan Arewa kana da miliyan Biyu a je amma dan makwabcinka dubu goma sha biyar ta hana shi zana jarabawa, ba a ma ta kudin rijistar shiga jami’a ko kwalejojin ilimi. Me yasa ba za mu taimaki ‘yan uwanmu ba, mu basu ilimi, amma sai dai mu barsu suna cen suna barace-barace da kuma cirani a Kudu kullum ana kashe su, ana cin zarafinsu ana wulakanta su, sai dai muji a kafafen sadarwa amma ba zamu iya daukar wani mataki na taimaka masu ba. Kusan fitattun masu kudin kasar nan a arewa su ke, wace rawa suka taka wajen magance barace-barace da yawon tazubar da matasan Arewa suke yi a kasar nan? Shin kamfunna na wa suka gina kuma matasa na wa suka dauka aiki a kamfunnan? Shin mu dukiyar arewa ba zata amfane mu ba, ya na da kyau masu hali na arewa su yi koyi da na kudu domin taimakawa matasansu, su dogara da kansu, ba wai su barsu cikin jahilci da bauta ba ga wadanda ba su gadewa.
A bangaren Matasan suma ya kamata su yi koyi da sauran matasa ‘yan uwansu na kudancin kasar nan wajen kirkira da kuma samar da wani sabon abu da zai taimake su. Arewa a kwai kasar noma, akwai yalwar wajen kiwo me zai sa matasan arewa ba za su tsaya su inganta rayuwarsu ba a arewa. ya kasance safara ce kawai zata kai su kudancin kasar nan. Me aka fi matasan arewa da ba za su iya kirkira ba, ba bu shakka a arewa a kwai hazikan matasa masu fasaha da kwazo, amma duk sun bar wannan kwazon ya tafi a banza, sai bangar siyasa da cirani da yawon maula da kaskantar da kai wajen da bai dace su yim haka ba.
A kudancin kasar nan sun cigaba wajen kirkirar abubuwan zamin da yawa, amma a arewa ko oho.
Gawamnatocin Arewa ya kamata ku tashi tsaye ku taimakawa matasan Arewa ta yadda duk wani abu da kuka bukata na cigaban yankin za su iya yi maku, misali Shugaban kasar Koriya ta Kudu, saboda yadda yake kyautatawa ‘yan kasar da kasar Amerika ta yi mashi barazana matasa sama da miliyoyi aka samu wadanda suka ce za su shiga sojan sa kai domin a yaki Amerika, wannan ya nuna cewa lallai sun a jin dadin shugabanninsu. Amma mu a nan arewa abun ya gagara wani abun ban haushi ko takaici ma shi ne in aka kashe wani dan arewa a kudu, sai ka ga wasu manyan arewa na ta tayar da jijiyar wuya, in aka nemi a yi ramuwar gayya, su ba su taimaki wadannan matasan ba kuma ba su taimamki kansu ba, wasunsu zaka ji suna cewa za su iya bayar da jininsu domin su taimaki yan kudu da ke arewa, amma ba zasu iya bada jininsu bas u taimaki ‘yan uwansu ‘yan arewa dake gida ma ba kudun ba, wannan ba karamin abun asha ba ne da koma baya, kuma irin wadanan shugabannin ba su arewa ke bukata ba a yanzu, domin ba su da wani amfani ga al’umma su dai ka barsu ga kare muradan kansu.
Amma har yanzu arewa bata makara ba zata iya gyara lokaci kuma bai kare mata sai ta tsaya tsaf ta natsu ta yi koyi da magabatan kwarai da a ka yi a baya, ya Allah a wannan kasar koma a wata kasar daban, domin bunkasa Arewa ta wuce tsara, domin Hausawa dai kan ce, Da na Gaba ake gane zurfin ruwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!