Connect with us

KIMIYYA

Miyagun Hanyoyin Mu’amala A Dandalin Sada Zumunci Na Facebook

Published

on

Wannan sabon tsarin mu’amala kuwa shi ne samuwar “Dandalin Sada Zumunci” ko “Dandalin Abota”, wato: “Social Media” ke nan a harshen Turanci. A karon farko mun gabatar da kasida ne kan Dandalin Facebook, mai take: “Dandalin Facebook a Mahangar Masana,” cikin shekarar 2010. Cikin jerin kasidun mun kebance wani bangare da muka yi wa take: “Manyan Badakala a Dandalin Facebook.” Wannan bangare yana dauke ne da labarai masu tayar da hankali, na takaici kan irin sakaci da halin ko-in-kula da jama’a ke yi wajen aiwatar da sadarwa a dandalin Facebook, wanda kuma hakan ya haifar da hasara ko salwantar dukiya ko mutunci a idon duniya. Kafin nan, naje rowa su matsaloli wajen guda 10 da ke tattare da dandalin facebook.
A shekarar 2013, 1 ga watan Janairu wata kungiyar tsangiyar alheri na matasan da ke dandalin Facebook sun gayyace ni taron su na shekara da suka yi a Katsina, inda na gabatar da kasida mai shafuka 14 mai take: “Rayuwar Matasan mu a Dandalin Abota.”Dukkan wannan kokari da yunkuri ne wajen fadakar da mu baki daya, don samun tsarin mu’amala mai tsabta a wannan mahalli mai cike da hadari.
To amma duk da haka, har yanzu da sauran rina a kaba. Abin nufi shi ne, a kullum ana samun karuwar masu mu’amala a wannan dandali. Sannan a kullum hanyoyi da tsarin wannan mahalli na sauyawa ne. A duk sa’adda ka dauki gajeren lokaci ba ka hau ba, da zarar ka hau sai ka ga wani abu sabo. kari a kan haka, akwai da yawa cikin mutane masu mugun nufi, wadanda ke amfani da jahilcin jama’ar da ke wannan dandali a duniya baki daya (ba wai a kasar mu kadai ba), da kuma sarkakiyar da ke tattare da manhajojin da ke, don cutar da jama’a ta hanyoyi daban-daban. Wannan ya sa na ga dacewar sake fadakar da mu don kara bude mana idanunmu, kar mu zama cikin wadanda za a kai mu a baro. Sannan, sabanin tsarin da na bi a baya, inda na takaitu ga dandalin Facebook kadai, a wannan karon zan duba hadurran da ke tattare da galibin ire-iren wadannan shafuka ne – Facebook, da Twitter, da Youtube, da Whatsapp da sauran makamantan su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!