Connect with us

WASANNI

Muhammad Salah Ya Kafa Sabon Tarihi

Published

on

Dan wasa Muhammad Salah ya sake kafa tarihi a Liverpool, bayan da ya ciwa kungiyar tasa kwallaye 3 a wasan gasar firimiya da suka fafata a karshen mako, wanda suka lallasa Bournemouth da kwallaye 4-0.
Kwallayen uku na Salah, sune cikon na 40 da ya ci wa Liverpool a wasanni 52 da ya buga mata, abinda ke nuni da cewa shi ne dan wasan kungiyar na farko da ya ci kwallaye masu yawa cikin wasanni kalilan.
A gefe guda kuwa, kwallaye ukun na Salah, sune na farko da wani dan wasan Liverpool ya ci, yayin da suka yi tattaki zuwa gidan wata kungiya, tun bayan irin bajintar da Luiz Suarez yayi a kungiyar cikin shekarar 2014.
A bangaren tarihin gasar firimiya kuwa, Alan Shearer da Andy Cole ne kawai suka samu nasarar zarta Muhammad Salah ta hanyar cin kwallaye 40 cikin wasanni 45 a tarihin gasar firimiya tun farkonta.
Tun bayan soma kakar wasan manyan gasannin nahiyar turai guda 5 a bara, Lionel Messi ne kawai ya zarta Salah wajen yawan kwallaye da 43, yayinda dan wasan na Liverpool ke da 42, sai kuma Harry Kane na Tottenham da kwallaye 39.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!