Connect with us

LABARAI

Rigakafin Cututtukan Yara Ya Samu Karbuwa A Karamar Hukumar Fagge

Published

on

Karamar hukumar Fagge tana matukar kokari da kula wa wajen ganin an sami bunkasar lafiyar al’ummarta ta bada gudummuwa da fannoni daban-daban.Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi ya bayyana haka da yake duba aikin riga-kafin cutar shan inna da sauran ctuka da suke damun yara a yankunan mazabun karamar hukumar.
Yace Gwamnatin Kano tana iya kokarinta wajen samarda allurori da magaunguna na riga-kafi na kauda cututtukan yara da sauran cutuka a tsakanin al’umma.Wanda su a Fagge suna iya bakin kokarinsu don tabbatarda cewa ana ayyukanda yakamata ayi na samun nasarar riga-kafinda ake ta jajaircewar ma’aikatan sashin lafiyar karamar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki.
Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi yace wannan nema yasa suke zagaya dukkan mazabu da Asibitoci da sauran cibiyoyi da ake yin riga-kafin don tabbatarda ana samun nasarar aikin riga-kafin.Kuma a Karamar hukumar ta Fagge basuda matsala ta samun cututtukan ko kuma ace ma’aikata basa aikinsu,suna samun kyakkyawan rahoto mai kyau na yanda ma’aikatan lafiya suke jajircewa wajen gudonarda aikinsu, ta irin ziyara da muke kai musu yana kara musu kwarin gwiwa sosai.
Ya yi nuni da cewa karamar hukumar Fagge da take kamar karamar Nijeriya da wahala wani abu ya taso na ci gaba kaga an bar su a baya ba su rungume shi ba saboda suna da wayewa da ilimi sun san yadda harkoki suke irin wadannan ba’a samun tirjiya a wajen amsar riga-kafi a duk lokacin da ake aiwatarwa.
Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi ya nuna godiyarsa ga al’ummar Fagge a kan wannan goyon ba ya da suke bashi tare da cewa nan kusa kadan akawai tsare-tsare da karamar hukumar take na raba magunguna ga Asibitoci don tallafawa samun lafiyar al’ummar yankin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!