Connect with us

LABARAI

Shugaban NIS Ya Wakilci Nijeriya A Taron Shige Da Fice Na Duniya

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice na Nijeriya, Muhammad Babandede ya wakilci Nijeriya a taron koli na duniya kan tabbatar da tsarin shige da fice mai inganci a duniya a Marakkesh da ke Kasar Moroko.
Muhammad Babandede wanda ya kasance kwararren masani kan harkokin shige da fice ya gabatar da kasida a kan matsayin Nijeriya game da shige da ficen kasa mara hadari, mai tsari da aka saba da shi.
Shugabanni daga kasashen duniya 164 sun amince a fito da sahihin tsarin da zai yaye wahalhalu da tarnakin da ake cin karo da su wurin shige da ficen kasashe a duniya, duk da adawar da wasu kasashe ke yi da hakan da kuma janyewa daga tsarin.
A ranar wannan Litini din ne aka gabatar da taron.
Yarjejeniyar da aka cimma a atron da ba a kai ga tsarawa a kundi daya ba ta hada da inganta tsarin shige da fice a cikin kasa da wajen kasa, da yankin kasashe da kuma duniya baki daya ciki har da rage hadurran da baki ko ‘yan gudun hijira ke fuskanta a zango daban-daban na tafiye-tafiyensu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!