Connect with us

KIMIYYA

Tasirin Kafafen Sadarwa A Harkokinmu Na Yau Da Kullum

Published

on

Masu bincike a a jami’ar Bristol dake kasar Birtnaiya, sun yi amfani da bayanai na sama da sakwanni Miliyan 800 da aka yada su a Twitter don auna yadda ake samun change- change na sama da awa ashirin da hudu.
Nuna damuwa data hada da yin fishi da yin murna, masu binciken sun nuna yadda soshiyal mediya kan samar da chanje- chanjea cikin rana da kuma sati da kuma lokutan kaka.
Binciken wanda shine na farko har ya zuwa yau, edtensibe study Dakta Fabon Dzogang ne ya jagoranci binciken kuma ya yi bincikenm ne tare da Farfesa Stafford Lightman da Farfesa Nello Cristianini wanda ya fito daga sashen kere-kere da lisassafi an kuma wallafa binciken nasu ne a mujallar Brain.
Jikin dan adama yakan samu yin kirdado a lokacin da ake da haske da kuma lokacin da ake cikin duhu a kowacce rana.
Dan wani karamin sanadari dake a cikin kwakwalwa da ake kira (suprachiasmatic) yana taimakawa wajen gudanar da ayyuka.
Haske yana taimakwa kwakwalwa sosai, musamman yadda zai taimaka mata wajen gudanar da ayyukan ta, har ila yau, yanayi yana taimakawa wajen sanya cin nasara akan abinda mutum ya sanya a gaba yake son cimma buri.
Masu binciken sun samo daga masu amfani da tweeter su milyan 800 dake kasar Birtaniya musamman akan wasu bayanai na tweeter 33,576 da aka yada sama da shekara hudu da suka wuce.
Sakwanni kamar na kalaman gaisuwa a wani lokacin da suka hada da, ina taya ka murna da barka da bikin Kirismeti da wannnan abun yanada kyau sa na bikin kiristeti dana sallar Easter dana sshigowar sabuwar shekara da sauran su, duk an fitar dasu don a kaucewa rikita bayananan.
Sakwanni da aka yada a tweeter anyi fashin baki akan su kalma baya kalma da suka hada dana nuna farin ciki da bakin ciki da nuna damuwa da kuma nuna jin gajiya.
Dakta Dzogang da abokan binciken sa, sun gano banbance-banbance na yanayin mutun mai kayu da maras kyau da yake ciki a sama da awa ashirin hudu na rana.
Masu binciken sun yi imanin cewar, wannnan binciken wannda shine karo na farko, ya rarrabe akan nuna damuwar da dan adam yakje ciki,inda take kowa fishi idan aka kwatan ta da lokacin da yake jin gajiya.
Masu binciken sun kuma gano cewar damuwa tana a kwance ne da safe, kafin a hankali ya karu da maraice.
Da safen yana kwance kamar da karfe shida hae zuwa karfe takwas na safen.
Ita kuwa gajiya, tana dagawa ce daga karfe takwas sai dai tana sauka sosai daga baya.
Yanayin jin walwala yana tashi ne da sauri da safe daga karfe takwas zuwa goma na safe da kuma zuwa karfe takwas na dare.
Yin amfani da kafar soshiyal mediya tana taimawa fannin kiwon lafiyar ‘yan adam.
Acewar Dakta Fabon Dzogang, wadannan dabarun da muka yi amfani dasu ta hanayar soshiyal mediya, sun taimakwa binciken mu wajen gano yanayin mutane da kuma dangantakar su.
Shi kuwa Frafesa Light man fata ya yi akan cewar za a yi amfani da binciken nasu don baiwa sauran kwarin gwaiwa yadda zau inganta kwakwalwalwar su da kuma kiwon lafiyar su ta hanyar soshiyal mediya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!