Connect with us

KASASHEN WAJE

Theresa May Ta Tsallake Yunkurin Sauke Ta Daga Mulki

Published

on

Firaye Ministar kasar Ingila, Theresa May, ta tsallake rijiya da baya, bayan da ‘yan majalisar dokokin kasar Ingila suka gudanar da kuri’ar amincewa da ita a matsayin shugabar jam’iyyar masu ra’ayin rikau da ke mulkin kasar ta Ingila.

Mafi yawan ‘ya’yan jam’iyyar masu ra’ayin rikau din da ke majalisar dokokin kasar Ingila sun kada kuri’ar amincewa da May din, inda ‘yan majalisa 315 suka kada kuri’ar amincewa da ita a matsayin shugabar jam’iyyar.

Inda yawan ‘yan majalisar sun kada kuri’ar rashin amincewa da May, da hakan zai sa ta sauka daga matsayin ta na shugabar jam’iyyar, sannan dole ta yi murabus daga mukamin firaye Ministar kasar ta Ingila din.

Wannan hauma-haumar ta biyo bayan rikicin da kasar Ingila ta fada a kokarinta na ficewa daga tarayyar Turai, wanda ake wa lakabi da “Brexit” inda mafi yawan ‘ya’yan jam’iyyar masu ra’ayin rikau din suke goyon bayan ficewar kasar Ingila daga tarayyar Turai din.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!