Connect with us

LABARAI

UNICEF Ta Bukaci Shugabannin Kasashen Duniya Da Su Kara Kaimi Wajen Kare ‘Yancin Yara

Published

on

A kwanakin baya ne asusun kula da yara na majaklisar dinkin duniya yayi kira ga shugabannin kasashen duniya kan su kara kaimi wajen kare ‘yancin yara. Wannan kira yana zuwa ne a yayin da duniya baki daya ta dauki amo a game da bukatar daidaikun mutane da su sanya hannu a cikin taskar da ake rubuta koke-koke ta shafin yanar gizo na bukatar samar da wani kudiri na musamman akan batutuwa da suka shafi yara, wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata takarda sanarwa wanda jami’in yada labaran ofishin UNICEF da ke Bauchi, Mr. Samuel Kaalu ya fitar.
“Muna bukatar gina wata duniya ce wadda kowane yaro zai kasance a makaranta, inda kuma rayuwarsa za ta samu kariya daga duk wani kalubale da kuma cika masu burinsu wanda babu wani wuri da ake bukata irin wannan yanayi sama da Nijeriya”, cewar wakilin asusun a Nijeriya, Mohammed Fall.
Sanarwar ta kara da cewa, “An cimma abubuwa da dama, to amma kuma akwai bukatar kara kaimi wajen tabbatar da cewar, yara a Nijeriya sun amfana da dokar kare ‘yancin su. A daidai wannan gaba, yara da dama ne aka tafi aka barsu a baya, don haka muke so mu cimmusu”.
Sanarwar ta kuma shaida cewar, Nijeriya ce take da adadi mai yawa na yara da basa halartar makaranta, haka kuma ita ce tafi adadin yawan mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara. “A kalla, fiye da yara miliyan hudu ne ba a yi masu rigakafin cutar shan-inna ba, haka kuma mutane miliyan goma ne suke gaza samun tsaftaceccen ruwa da muhalli a Nijeriya, wanda hakan yana sanya lafiyar yara cikin hatsari,” Kamar yadda bayanin manema labarum ya ce.
A cewarsa, cututtuka kamar cuta mai toshe kafofin numfashin yaro (Pneumonia) da gudawa hadi da cutar zazzabin cizon sauro, da kuma karancin abinci mai gina jiki suna silar mutuwar yara a Nijeriya.
“Nijeriya ce ta biyu a duniya da aka fi haifar kananan yara wadanda suke fama da matsalar abinci mai gina jiki, inda a cikin wata kididdiga da aka yi an gano cewar, yara miliyan goma sha shida da digo biyar (16.5m) aka haifa wanda miliyan biyu da digo shida (2.6m) suke fama da cutar tamowa.
“Imma dai ako ina ne aka haifi yaro, wala-Allah iyayensa masu wadata ce koko akasin haka, shi da iyayensa suna da kyakkyawan fatan ganin makoma nagari. Don haka muke bukatar kowane yaro ya samu damar gudanar da rayuwa mai ‘yanci da kuma ganin mafarki da aka yi ya zama gaskiya”, cewar Mohammed Fall.
Mohamammad Fall a cikin bayanin manema labarum ya kuma kara da cewa, “Tare da aikin hadin gwiwa da gwamnatin Nijeriya mun himmatu domin tabbatar da cewar, mun zuba babban jari da zai haifar da kyakkyawan sakamako ga dukkan yara a fannonin ilimi, kiwon lafiya, ciki har da kawar da cutar shan-inna, cutar tamowa da kuma samarwa yara kariya”, kamar yadda sanarwar ta yi nuni.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!