Connect with us

MANYAN LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 22 A Zamfara

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kashe mutum 22 a kauyen Malikawa dake yankin Gidan Goga na karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Mutanen garin sun bayyana wa manema labarai cewa, ‘yan bindiga da dama ne dauke da muggan makamai a kan babur suka mamaye kauyen inda suka shiga harbe-harbe ba kakkautawa.
“Na dawo daga gona ne da misakin karfe 4, na yi shawarar yin wanka, ina cikin ban dakin ne sai naji mutane na ta ihu, fitowa ta ke da wuya sai na ga gaba daya garin ya hargitse, ana ta ihu.
“Mutane na ta guje-guje, yara da manya na ihun neman taimako, a nan ne fahinci muna cikin mummunan hari, sun ci gaba da bin mutane suna kashe wa, sun a bin su a kan babur suna kashe wa.
“Ina kokarin neman inda zan tsira sai kawai na ga ‘yan ta’addan a bakin kofar gida na, har zuwa yanzu bansan yadda Allah ya tsirar da ni ba,” inji wani mazaunin kauyen.

Ya kuma kara bayyana cewa, an kona mutum 6 da ransu suka kuma lullubesu a cikin karmamin dawa a bayan gari.
“Lokacin da suke bin mutane a kan mashin wasu mutum 6 suka lullube kansu a cikin karar dawa, ashe ‘yan ta’addan sun gansu sai kawai suka banka wa karmamin dawar wuta, inda mutum 6 dake cikin suka kone kurmus.
“Maganan nan dana ke yi maka, ina kauyen Boko ne wajen neman yaran da bamu gansu ba, wadanda kuma suka mutu mun riga mun birne su,” inji shi.
Duk koarin jin ta bakin Jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu a kan lamarin kafin hada wannna rahoton ya ci tira.
Idan za a iya tunawa yankin na Gidan Goga ya sha fuskantar hare haren ‘yab ta’adda a kan Babura inda suke kashe mutane a duk lokacin da suka kawo harin.
Haka kuma, a harin ranar Litinin an kashe jami’an tsaro ‘yan sa kai na farin kaya, aka kuma kame wasu matan aure biyu, matan tsohon shugaban karamar hukumar Shinkafi, Bello Birnin Yero da kuma diyarsa duk a garin Shinkafin ta Jihar Zamfara.
Majiyarmu ta kawo rahoton wani da lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Isah Adamu, yana cewa, ‘yan ta’addan sun zo ne su sama da 100 suka yi wa garin kawanya da misalin karfe 12 na dare, inda suka shiga gidan dan siyasan suka yi awon gaba da diyarsa da kuma matan na shi biyu.
“A lokacin da aka sanar da ‘yan kungiyar sintirin, nan take suka kawo dauki inda suka bi sawun ‘yan ta’addan da nufin kwato matan. A musayar wutan da suka yi ne, ‘yan ta’addan suka kashe ‘yan sintirin uku, suka kuma tsere tare da matan uku.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta agaza masu wajen turo Sojoji a yankin na su domin samar da zaman lafiya.
Muna fuskantar barazana sosai daga ‘yan ta’addan masu dauke da muggan makamai a kullum, muna bukatar karin jami’an tsaron da za su farmake su a maboyar su. Domin suna kusa ne da mu a kan iyakan mu da kasar Nijar,” in ji shi.
Kokarin mu na yin magana da Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ta Zamfara, Muhammad Shehu ya ci tura a zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A watan da ya wuce ne, Gwamna Abdulaziz Yari, ya amince da daukan ‘yan sintiri 8,500 aiki a kananan hukumomin Jihar 17 domin su taimaka wajen yaki da ‘yan ta’addan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!