Connect with us

KASASHEN WAJE

Yarjejeniyar Kariya Ga Baki Masu Kaura Ta Samu Sa Hannun Kasashe 150

Published

on

Taron Majalisar Dinkin Duniya kan yadda za a inganta kula da bakin da ke kaura tsakanin kasashe a Morocco ya amince da wani shiri a gaban shugabannin da wakilan kasashe kusan 150 duk da janyewar da wasu kasashe suka yi.
Ita wannan yarjejeniya da wakilan kasashe kusan 150 suka amince da ita a Marakesh da ke Morocco, an yi mata lakabi da shiri na musamman domin kare baki da tabbatar da tafiyar su cikin yanayi mai kyau, wanda aka kamala tantance shi bayan tarurrukan da aka kwashe watanni 18 ana yi.
Yarjejeniyar ta gindaya sharidodi 23 na samun halartacciyar kaura da kuma haramta ketare iyaka ba tare da bin ka’ida ba, ganin adadin bakin da suka kaura ya zarce miliyan 250 yanzu haka.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterress ya bayyana yarjejeniyar samar da kariyar ga bakin hauren a matsayin mafita guda da za ta kawo karshen kalubalen da ‘yan ciranin kan fuskanta.
Guterres ya ce abin kunya ne asarar rayukan da ake samu musamman akan hanyar bakin hauren ta yin kaura zuwa nahiyar Turai don samun ingantacciyar rayuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!