Connect with us

LABARAI

Yau Kungiyar ASUP Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

Published

on

Kungiyar malaman kwalejojin Kimiyya da Fasaha na kasar nan ta fadi a ranar Talata cewa, ba gudu, ba ja da baya a kan shigar ta yajin aikin sai baba ta gani, da ta shirya tsunduma a ciki a ranar 12 ga watan Disamba a duk Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa, Mista Usman Dutse, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da ya yi da kamfanin Dillancin labarai na kasa.
Dutse ya ce, shigan su yajin aikin ya zama tilas a bisa yanda gwamnatin tarayya ta kasa aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a tsakanin su a shekarar 2009 da kuma 2017.
Ya ce, “A gobe ne za mu fara yajin aikin namu kamar yanda muka tsara. Mun kammala shirya komai, ba fashi.
“Akwai gayyatar da aka yi mana domin tattaunawa a ranar 17 ga watan Disamba, amma duk da hakan za mu fara yajin aikin a ranar ta Laraba, (Yau kenan).
“Ban san ko mai zai faru ba a wajen tattaunawar, ko kuma abin da suke da niyyar yi, sai dai mun zauna, ba ma iya cewa ga abin da zai faru.
Dutse ya ce, yajin aikin ya zama tilas har sai gwamnati ta warware matsalolin a cikin kasa baki-daya.
Ya ce, kungiyar ta baiwa gwamnati wa’adi, inda kuma ta bukaci duk wakilanta na kasa da shiga yajin aikin tun daga daren ranar 12 ga watan Disamba.
Shugaban ya ce, shugabannin kungiyar za su sake aikewa da tunin hakan ga duk sassan su, ya kara da cewa, ba malamin da zai kara daukan allin rubutu a duk Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na kasar nan, har sai abin da hali ya yi.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!