Connect with us

MANYAN LABARAI

Za Mu Fallasa Sunayen Gwamnonin Da Ma’aikata Ke Bi Bashi –NLC

Published

on

Kungiyar kwadago ta kasa tare da hadin gwiwar kungiyoyin kwadago na Duniya wajen shelanta sunayen gwamnonin Jihohin da Ma’aikata ke bi bashin kudaden albashi da kudaden Fensho na tsawon watanni.
Kungiyar kwadagon ta Duniya ita ce babbar kungiyar kwadago ta Duniya.
A 1 ga watan Nuwamba, 2006 ne aka sami gamayya a tsakankanin kungiyoyin kwadago na Duniya wajen kafa kungiyar.
Shugaban kungiyar kwadagon, Ayuba Wabba, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a taro na17 na masu karban Fensho ranar Talata a Abuja.
Ya bayyana cewa, “Baya ma ga shelanta sunayen na su da kuma kunyata su,” kungiyar ta NLC za ta umurci ma’aikatan kasar na da su sanya ido a kan irin wadannan gwamnonin a dukkanin tashoshin Jiragen sama na kasar nan domin kar su tsere daga kasar bayan sun kammala wa’adin mulkin na su.
Ya ce, a maimakon su yi amfani da kudin wajen kyautata rayuwar al’umma, su gina kasan da za ta yi dadi ga kowa, sai kawai wasu ‘yan kalilan su yi facaka da kudin al’umma a kashin kansu.
Daganan Wabba ya tabbatar wa da masu karban Fenshon cewa, NLC ba za ta sarara ba har sai ta tabbatar da an biya mafi karancin kudin Fensho a tare da mafi karancin albashi.
Wabba, ya yabawa Shugaba Buhari, a kan kokarin da ya yi na biyan basukan baya da masu karban Fensho na ma’aikatan hukumar Jiragen sama na kasar nan na karin kashi 33.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!