Connect with us

MANYAN LABARAI

Allah Ya Yi Wa Shaikh Tijjani Kalifa Zaria Rasuwa

Published

on

Allah ya yi wa Shehin darikar Tijjaniya, kuma babban mukaddamin darikar ta Tijjaniyya, dake zaune a Zaria, Shaikh Tijjani Khalifa rasuwa, shehin ya riga mu gidan gaskiya ne bayan wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya, marigayin ya bar duniya yana da shekaru 73 a duniya.

 

Dan uwan marigayin, Shaikh Sani Kalifa ne ya sanar da rasuwar Shehin a jiya Laraba da yamma a garin Zaria dake jihar Kaduna, kafin rasuwar shehin yana daga cikin ‘yan kwamitin amintattu na kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam ta kasa.

Marigayin mai shekaru 73, ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 32, yau aka gudanar da jana’izar sa kamar yadda addinin  musulunci ya tanada a babban masallacin juma’ar gwargwaje dake garin Zaria, da misalin karfe biyu da rabi na ranar yau Alhamis, Allah ya ji kanshi Allah ya mishi gafara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!