Connect with us

MANYAN LABARAI

Ba Mu Ayyana Buhari A Matsayin Dan Takarar Da Za A Zaba Ba –Kungiyar CAN

Published

on

Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), ta karyata rahotannin da suke cewa kungiyar ta ayyana shugaban kasa Buhari a matsayin dan takarar da za a zaba a zabukkan shekarar 2019, kungiyar ta ce ayi watsi da irin wadannan rahotannin na karya da suke yawo a shafukkan labarai na intanet.

Kungiyar ta ce ba ta ayyana wani dan takara a matsayin wanda za a zaba ba, duk da tayi zaman tattaunawa a ranar Litinin da ‘yan takarar shugabancin kasa su 14, hakan ba yana nufin ta ayyana wani dan takara a matsayin dan takarar da za a zaba bane, don haka a kiyaye da irin wadannan rahotannin.

Kungiyar ta ce ta yi zama ne da ‘yan takarar don jin tsare-tsaren da suke da shi na ci gaban kasa, sannan sam maganar ayyana ko amincewa da wani a matsayin dan takara bai ma taso ba a zaman tattaunawar, don haka kungiyar ta bukaci al’umma ta yi hankali da masu yada irin wadannan rahotannin na karya marasa tushe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!