Connect with us

KASASHEN WAJE

Dan Shekaru 11 Mai Suna Trump Ya Bukaci A Canja Mishi Suna Saboda Ana Yawan Tsokanar Shi

Published

on

Wani yaro mai suna Trump, dalibin makarantar firamare mai shekaru 11, ya bukaci a canja mishi sunan shi, saboda a cewarshi sunan ya jawo mishi tsokana da musgunawa daga yara ‘yan uwanshi, mahaifiyar yaron, Megan Berto ta ce dan nata yana matukar fuskantar musgunawa da tsokana daga ‘yan makarantarsu saboda sunan Trump da yake cikin jerin sunayen shi.

‘Suna yawan la’antarshi, suna kiranshin sakarai, suna ce mishi wawa da sauran kalaman zagi da batanci, wasu lokutan har bugun shi yaran suke yi, saboda kawai akwai Trump a sunan shi, wannan lamarin ya yi kamari, har rayuwar dana ta shiga cikin kunci saboda sunan Trump kawai dake cikin sunan shi.’ Inji Megan Berto

Megan ta ce dan nata bashi da wata alaka da shugaban kasar Amurka Donald Trump, a shekarar da ta gabata sai da ta kai an cire yaron daga makaranta, inda aka mayar da shi gida ya ci gaba da daukar darasi a gida, amma duk da haka abun bai canja ba, bayan shekara daya an ci gaba da musguna mishi.

Iyayen yaron sunyi kokarin sanar da malaman makarantar da yaron yake, da jami’an tsaro ma dukka, amma abun bai canja ba, yaron ya ce duk sun sa ya tsani kanshi, sannan ya tsani wannan sunan Trump, yaron ya ce gaba daya duniya bata mishi dadi, bai son ma ya tuna akwai sunan Trump a jerin sunayenshi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!