Connect with us

KIMIYYA

Kamfanin Sadarwa Na Vodacom Za Ta Horar Da Dalibai A Legas

Published

on

Kamfanin ‘Bodacom Business Nigeria’ ya kammala dukkan shirin da ya kamata na horar da daliban makarantun Sakandire a jihar Legas a kan fasahar ilimin kimiyyar sadarwa.
Makasudin wannna shirin, kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga hukumar kamfanin ya bayyana shi ne samar da masana da za su taimaka wa Nijeriya a yayin da ake fuskantar juyinjuya hali da ke aukuwa a bangaren kimiyya da fasaha a fadin duniya a hakun yanzu.
A wannan shirin horarsa na rana daya a kan fasahar ‘robotics’, kamfanin na Bodacom, ya bayyana cewa, an shirya ba daliban horo a kan yadda za su kikiro manhajar da za su iya saffara su don taimakon mutane, ta yadda za a samu ci gaba wajen kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu gaba daya. Da yake tsokaci a kan wannna shirin, shugaban bangaren kasuwanci na kamfanin, Solomon Ogufere, ya yi bayanin cewa, “A matsayinmu na kamfanin kasuwanci, mun dauki aniyar samar da dalibai da za su kasance kashin bayan Nijeriya a shekaru masu zuwa a bangaren kimiyya da fasaha, musamman ganin juyinjuya halin dake tafe a bangaren masa’anantu a fadin duniya.
“Mun yi imanin cewa, bamu makara ba kuma bamu yi gagawa a kokarin ganin mun samar da dalibai masu ilimin kimiyya da fasaha, ilimn da za a bukata a shekaru masu zuwa, in har ana son Nijeriya ta kasance a cikin kasashen duniya masu ci gaba.”
Kamfanin ta kuma bayyana cewa, makarantun da suka shiga cikin wannan shirin sun hada da Dansol High School, Ikeja da Edgefield College, Lekki da Fruitful Bille College International, Ikorodu da Halifield Schools, Maryland da kuma Holy Child College, Ikoyi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!