Connect with us

MANYAN LABARAI

Kin Bin Umurnin Kotu: Dasuki Ya Kalubalanci Ci Gaba Da Shari’arsa

Published

on

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta sake daga shari’ar da ake yi wa tsohon mai baiwa tsohon Shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, har sai ranar 9 ga watan Janairu, 2019, bayan ya yi tambaya a kan hakkin da kotun ke da shi na ci gaba da sauraron shari’ar na shi, duk da kin da gawamnatin tarayya ta yi na bin umurnin kotu, na sakin sa.
Alkalin kotun, Ahmed Muhammed, ne ya dage sauraron shari’ar a ranar Talata, bayan da Lauyan da ke kare wanda ake kara ya yi magana a kan cancantar da kotun ke da shi na ci gaba da sauraron shari’ar ta Dasuki.
Lauyan na Dasuki ya ce, suna son ne a dage sauraron shari’ar har sai ranar da gwamnatin tarayya ta bi umurnin da kotu ta yi a ranar 2 ga watan Yuli, inda ta bayar da umurnin sakin Dasuki din ba tare da bata lokaci ba.
Babban Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ya ce, gwamnatin tarayya ba za ta saki Dasuki din ba.
A zaman da Kotun ta yi na ranar 19 ga watan Nuwamba, ne kotun ta dage shari’ar har zuwa ranar Talatan nan.
Ana kiran shari’ar ne a ranar ta Talata, sai Lauyan da ke kare wanda ake karan, Adeola Adedipe, ya ce ai sun shigar da wata bukata a gaban kotun.
“Bukatar wacce aka gabatarwa kotun a ranar 11 ga watan Disamba, mai dauke da kwanan watan 10 ga watan na Disamba, ya kamata a saurare ta ne a maimakon ci gaba da sauraron shari’ar, saboda bukatar tana magana ne a kan hurumin da kotun ke da shi na ci gaba da sauraron ita kanta shari’ar.
Da yake mayar da martani, Lauya mai gabatar da kara, Oladipupo Opeseyi, ya shaida wa kotun cewa, tabbas ya karbi kwafin bukatar da wadanda ake karan suka shigar a ranar Talata din da safe a lokacin da ya iso kotun, amma bai kai ga duba abin da ta kunsa ba.
Oladipupo Opeseyi, ya ce abin da dai ke gaban kotun a ranar shi ne ci gaba da sauraron shari’ar.
Sai dai, Mai shari’an, Muhammed, ya amshi bukatan Lauyan da ke kare wanda ake kara ne, inda ya sanya sauraron bukatar na su a gaba a maimakon a ci gaba da sauraron shari’ar.
“In har wannan kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar duk da wannan halin da ake ciki, hakan ya nuna ta ci amnar bukatar da aka shigar ne a ranar 11 ga watan Disamba. A bisa ga dukkanin alamu, wanda ake kara yana tuhumar wannan kotun ne a bisa ikon da take da shi na ci gaba da sauraron shari’an na shi, kamar yanda babban Lauya ya nu na.
“In har kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar a yau din nan, wannan ya nuna ta rigaya ma ta yanke hukunci kenan a kan cewa iyi, tana da ikon ci gaba da sauraron shari’ar.
“Kotun ce ya fi dacewa da ta duba ko wannan bukatar da aka gabatar mata tana da wani nauyi ko ba ta da shi. A kan haka, Kotu za ta sanya wataranar domin sauraron ita wannan bukatar.”
A nan ne sai Mai shari’an Muhammed, ya dage zaman har zuwa ranar 9 ga watan Janairu, domin a saurari bukatar na su.
Tun a shekarar 2015 ne aka kama Dasuki, yake kuma tsare duk da umurnin da kotuna suka bayar na a sake shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!