Connect with us

KASASHEN WAJE

Kotu Ta Yankewa Dan Sandan Da Ya Yi Wa ‘Yar Shekaru 13 Fyade Shekaru 25 A Gidan Yari

Published

on

Wata kotun kasar Ingila ta daure wani jami’in dan sandar kasar, bayan da kotun ta same shi da laifukka har guda 37, ciki da har da laifin yi wa yarinya ‘yar shekaru 13 fyade a cikin motarshi.

Dan sandan ya shaidawa mai shara’a cewa da sanin yarinyar ya sadu da ita, kuma lallai ta ji dadin saduwar, dan Sandan mai suna Ian Naude, wanda yake aiki da sashen yan sanda masu lura da tsagerun yara.

Dama ana zargin jami’in da aikata laifukka da suka shafi fyade, kotun ta gano jami’in ya ziyarci gidansu yarinya har sau uku, ziyarar shi ta karshe itace wacce yaje bincikar wata hatsaniya da ta faru a gidansu yarinya, kwana uku kafin faruwar lamarin.

Jami’an ya jawo yarinyar zuwa cikin motar shi da karfin tsiya inda ya yi mata fyade, kotun ta zarge shi da yin amfani da matsayinsa na jami’in ‘yan sanda wajen yi wa yarinyar fyade, inda mai shara’an ya yanke mishi wannan hukunci a take bayan an same shi da laifukkan da ake tuhumarshi da aikawata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!