Connect with us

MANYAN LABARAI

Kotu Ta Zartarwa Dan Shekaru 24 Da Ya Kashe Surukarshi Hukuncin Rataya      

Published

on

Babbar kotun jihar Filato da ke zama a garin Jos, ta zartarwa wani mutum dan shekaru 24, mai suna Binfa Lamde, hukuncin rataya, bayan da kotun ta same shi da laifin kisan gilla ga surukar shi a yau Alhamis.

Mai shara’a A. I Ashoms wanda ya jagoranci zaman shara’ar, ya ce duk shaidu sun tabbatar da cewa Binfa Lamde ne ya yi wannan kisan, tabbas Lamde ne ya kashe Kum Zwede, kuma kisan rashin imani da tausayi ya yi mata wacce surukar shi ce.

‘Dukkan shaidu sun tabbatar da cewa Lamde ne ya aikata wannan danyen aikin, don haka wannan hukunci da aka zartar mishi ya zama wajibi, bisa la’akari da tanadin dokar kasa, duk wanda ya yi kisan kai da gangan, hukunci shi rataya ne.’ inji Mai shara’a Ashoms

Ashoms ya kara da cewa: Don haka hukuncin da ya hau kan Lamde shine za a rataye shi har sai ya mutu.

An gurfanar da Lamde ne tun a ranar 14 ga watan Yulin shekarar 2014, bayan da ake zargin shi da yin kisan gilla ga surukar shi mai suna Kum Zwede, Lamde ya kashe surukar tashi ne a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2014, inda ya yi amfani da adda wajen daddatsa surukar tashi.

Lamde ya ce ya kashe surukar tashi ne bayan da suka gano surukar tashi mayya ce, kuma har ma ta kama kuruwar kanwar Lamde din, sun yi sunyi da ita ta sake kuruwar yarinyar, amma ta ki, daga baya yarinyar ta mutu, sannan dan Lamde din shi ma ya kamu da irin rashin lafiyar da kanwar Lamde din ta yi kafin ta mutu.

Lamde ya ce wannan ne ya sa ya hasala har ya sa ya shiga dakin surukar tashi a daidai lokacin da take bacci, inda ya sassara ta da adda har sai da ta mutu, amma lauyan Lamde din ya ce duk da hukuncin da kotun ta yi daidai ne, amma yana ganin za su daukaka kara anan gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!