Connect with us

MANYAN LABARAI

Ministan Muhalli Ya Yi Murabus Don Zama Sarkin Nasarawa

Published

on

A halin da ake ciki Ministan Muhalli, Ibrahim Jibrin, ya yi murabus daga majalisar zartaswar Nijeriya, murabus dinsa ya biyo bayan nada shi ne da aka yi a matsayin Sarkin Nasarawa na 12 dake jihar Nasarawa
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da murabus din a taro majalisar da aka gudanar jiya Laraba a fadar Shugaban kasa dake Abuja.
Day ake jawabin ban kwana ga majalisar, Mista Jibrin ya tuna cewa, a yayin da yake Minista, ya samu daman zagaye tarayyar kasar nan inda ya lura da gaggarumin barnar da canjin yanayi da kuma yakin dake gudana da ‘yan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas suka ga rayuwar jama’ar yankin da muhalli gada daya.”
Ya ce, a yankin Kudu maso Kudu kuma ya gani da idonsa “In da danyen mai ya mamaye albarkatun ruwa kamar su kife da ake dasu, hakan ya karfafa masa niyyar aiki da wannna gwamnatin don dakatar da gurbatar yanayi da kuma bukatar share dagwalon mai a yankin Ogoni da kuma jihar Ribas.
“Gobe 13 ga watan Disamba a kwai taro a Fatakwal in da za a mika wa ‘yan kwangila wurin da za su gudanar da ayyukan share dagwalon man da ake fama dashi.
A lokuttan baya kafin wannan gwamnatin, kamfanonin mai sun ki bayar da kudaden gudanar da ayyukan amma kokarin wannan gwamnati ya sa yanzu sun biya fiye da Dala Miliyan180.
Ya kuma kara da cewa, share dakwalan mai na yankin Ogoni yana cikin babban aikin da ma’aikatar Muhalli ke gudanarbwa kuma sun ki yarda a rarraba kudaden kamar yadda ake yi a shekarun baya, an yi haka ne don kada aikin ya samu matsala kamar yadda saura ayyukan suka fuskanta a lokuttan baya.
Ya ce, a kwai wuraren da zaizayar kasa ta shafa fiye da 400 a yankin jhar Anambara, a kan haka ya bukaci gwamnonin jihohi su yi amfani da kudaden shawo kan zaidaiyar kasa da kwamnatin tarayya ke bayarwa yadda ya kamata maimakon barin matsalar ga gwamnatin tarayya.
“Ina kira ga abokan aikina su ci gaba da bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya har sai an samu nasarar day a kamata,” inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!