Connect with us

MANYAN LABARAI

Obasanjo Ya Rude, Ba Mai Kallonsa Da Kima -Fadar Shugaban Kasa

Published

on

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kalaman tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya yi kwanan nan, tana mai cewa, kalamai ne na wanda ya rude da bai kamata a mayar da hankali a kansa ba.
Da yake jawabi ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba, jami’in watsa labarai na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ce, duk wanda Mista Obasanjo ya zabi ya goya wa baya a zaben 2019 ba shi da wani mahimmanci don ya yi ta canza matsaya a ka haka a cikn ‘yan watannin nan da suka wuce kawai.
“A yau tsohon shugaban kasa Obasanjo na goyon bayan wannnan gobe kuma yana goyon bayan wannnan.
“In ya ga dama sai ya sa Allah a kan dalilin goyon bayan wannnan, yana kuma amfani da wani dalili kuma na goyon bayan wani dan takarar kuma,” inji shi.
Mista Shehu ya kuma kara da cewa, bai yi mamaki ba da jaridu suka ruwaito Mista Obasanjo ya na bayyana matsayinsa na dan ba ruwansa a kan goyon bayan dan takara ba a zabe mai zuwa, sai kuma bayan kwana daya ko biyu ya sake bayyana wata matsayar gaba daya.
“Tuni muka tsayar da shawarar watsi da shi tare da rashin daukarsa da mahimmanci.
“Muna da tabbabacin cewa, dan guguwa kada za a sake samu ya canza matsayarsa kuma, in za a a iya tunawa wannnan ne fa mutumin da ya ya ga takardar ragisatarsa na jam’iyya a bainar jama’a shekaru hudu da suka wuce sai kuma ga shi yau ya koma yana goyon bayan jam’iyyar,” inji Mista Shehu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!