Connect with us

MANYAN LABARAI

Oshiomhole Ya Musanta Zargin Caccakar Aisha Buhari

Published

on

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya musanta cewa ya yi wasu munanan kalamai a kan Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, a kafafen yada labarai na yanar gizo.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ta hannun babban Sakatarensa na yada labarai, Simon Ebegbulem, cewa ya yi, wannan aikin wasu ne masu nufin hada wuri, yana kuma daga cikin labaran zuki-tamalle da wasu ‘majigatan Jam’iyyar PDP ke yadawa.’
Mun jiwo wasu munanan kalamai da ake karyan cewa Shugaban Jam’iyyar APC, Oshiomhole, ne ya fade su, a kan Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, a kafafen yada labarai na yanar gizo.
“Muna bayyana cewa, wannan aikin masu son hada wuri ne kawai. Ba inda shugaban Jam’iyyar na APC ya fade su a kan Uwargidan ta Shugaban kasa.
“Wannan duk suna cikin irin labaran karyan da manyan Jam’iyyar PDP ke yadawa, a lokacin da suka tabbatar da cewa, sun fadi a babban zaben da ke tafe.
“Abin takaici ne ga ‘yan Jam’iyyar ta PDP, duk wasu kulle-kulle da suka yi na watsa hadin kan ‘yan Jam’iyyar APC ya ci tura. A maganan nan da muke yi a halin yanzun, Uwargidan ta Shugaban kasa, Oshiomhole, da sauran shugabannin Jam’iyyar ta APC suna dasawa a tsakanin su domin tabbatar da cewa barayin Jam’iyyar PDP ba su komo kan mulkin kasar nan ba.
“Muna bukatar al’ummar kasar nan da su yi watsi da wadancan kalamai na batunci da ke yawo a kafafen yada labarai na yanar gizo, domin duk ba gaskiya ne ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!