Connect with us

FITATTUN MATA

Amina Mohammed: ‘Yar Nijeriya Ta Farko Da Ta Zama Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Published

on

Ko-kun-san?
A yau filin namu na ‘fitattun mata’ na dauke muku da tarihin rayuwar wata jaruma wacce yanzu haka ita ce mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya wato Amina J. Mohammed. Fitacciyar ta taka muhimman matakai a rayuwarta wacce sunanta ya cilla a duniyar nan, inda kasar nan take alfahari da ita. Jajirtacciyar mace ce mai kokarin samar wa jama’a hanyoyin fita daga radadin talauci, ta zama Ministar muhalli a Nijeriya a karkashin gwamnatin Buhari. Amina ta kasance mai bayar da shawarwari kan muhimman abubuwa ga kungiyoyi daban-daban a fadin duniya. Yanzu haka, Amina tana daga cikin ‘yan Nijeriyar da fitilarsu ke haskawa a wannan duniyar.

Wace ce Amina Jane Mohammed?
An haifi Amina Mohammed ce a ranar 27 ga watan Yuni ta shekarar 1961 a jihar Gombe. Ta yi makarantar Firamare a kasar Amurka, sannan ta halarci kwalejin Henley Management a shekarar 1989, bayan ta kammala karatunta a kasar Italiya sai mahaifinta ya dawo nan gida Nijeriya.
A tsakanin shekarar 1981 da 1991, Amina Mohammed ta yi aiki a Archcon Nigeria- Norman da kuma aiki da Dawbarn United Kingdom a shekarar 1991. Ta samu nasarar kafa Kamfanin Afri-Projects Consortium, daga shekarar 1991 zuwa 2001.
Daga shekarar 2002 har zuwa 2005, Amina Mohammed ta kasance mai gudanar da gangamin wayar da kai kan jinsi da kuma ilmantarwa a karkashin shirin cimma muradin karne a majalisar dinkin duniya.
Daga bisani Amina ta zama babbar mai taimaka wa shugaban kasar Nijeriya kan shirin cimma muradin karni na ‘Millennium Debelopment Goals (MDG’s)’.
A shekarar 2005 ne ta kasance mai kula da asusun kula da rage radadin talauci a Nijeriya a cikin shirin MDG’s. A wannan zangon ta taka rawa sosai wajen samar da tsarin da ya ba da damar rage talauci a tsakanin jama’a, ta fuskancin kasafi da bibiyar kudaden da aka ware domin taimaka wa mutane kan yaki da talauci. Ta kuma tabbatar da cewar kudaden suna shiga hanun wadanda aka ware dominsu don ganin an cimma muradin da aka sanya a gaba. Daga bisani ta sake samun zarafin samar da wata cibiyar ci gaba da samar da mafita ga jama’a mai suna ‘Center for Debelopment Policy Solutions’.
A wancan lokacin Amina ta kasance mamba mai bayar da shawarwari a kungiyoyi daban-daban ciki har da kungiyoyin kasa da kasa, kai har ma da mambar da ke bayar da shawara ga sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan shirin ciyar da jinsi gaba a shekarar 2015, sannan ta kasance a cikin kungiyoyin kan tabbatar da muradin karni daban-daban. Ta taba shugabantar masu bayar da shawara kan shirin UNESCO domin bibiyar hidimar ilimi a duniyance (GME).
Daga shekarar 2012 Amina ta kasance cikin mutane masu fada-a-ji, domin ta kasance mai bayar da shawara ga sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a shekarar 2015. A wannan lokacin ta samu kulla alaka sosai da Majalisar Dinkin Duniyar kan shirye-shirye da dama da suka hada da (HLP), (OWG), da dai sauransu.
Ta yi murabus daga cikin majalisar zartaswar gwamnatin Buhari ne a ranar 24 ga watan Fabrairun 2017. Har ila yau, a watan Janairun 2017 ne dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sanar da zabar Amina Mohammed a matsayin mataimakiyarsa wanda har zuwa wannan lokacin ta ke kan wannan kujerar.
Kungiyoyin da ta bayar da gudunmawa a cikinsu:
Amina Mohammed ta shiga cikin wasu kungiyoyi daban-daban ta kuma taka rawa domin ci gaba, wasu daga ciki ta kasance mamba a sashin Daraktoci na hadakar kawancen ci gabata ta ‘Global Partnership for Sustainable Debelopment Data’ tun a shekarar 2017, sannan, ta kasance mamba mai bayar da shawara a kan aikin jin kai na Action Aid. Ta sake zama mamba mai bayar da shawara a Gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, mamba ce a Hewlett Foundation, mamba ce a cibiyar International Debelopment Research Centre, sannan ita mamba ce da ke bayar da shawara a Tsangayar Tattara Bayanan Kimiyya da Kere-kere “Institute of Scientific and Technical Information of China (ISTIC)”.
Lambobin yabon da ta samu a rayuwarta:
Amina Mohammed ta amshi lambobin yabo masu tarin yawa, kadan daga ciki, a shekarar 2006 ta samu lambar yabo ta karramawa daga Nijeriya ta ‘National Honours Award’. A 2007 ta samu wani lambar yabo ta ‘Nigerian Women’s Hall of Fame’ kana ta taba samun wata lambar yabo kan ciyar da al’umma gaba da kuma tausaya musu ta ‘Ford Family Notre Dame Award for Internatinon Debelopment and solidarity a shekarar 2015, kana da lambar yabon da ta samu a shekarar 2017 ta Jami’ar Difilomasiyya ‘Diplomat of the year Awards 2017’ da dai sauransu.
A baya-bayan nan, Amina Mohammed Mataimakiyar babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ta shiga sahun mata uku rak fadin Nijeriya da suka samu zarafin fitowa a cikin cikin kundin jerin zaratan mata na duniya guda 100, wanda kafar yada labarai ta BBC ta ware a wannan shekarar ta 2018.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!