Connect with us

HANTSI

Dabarar Kubuta Daga Masu Satar Mutane Ta Wayar Hannu

Published

on

Da yawan mutane suna siyan wayoyin hannu ne ba don abun da wayoyin suka kunsa ba, sai don ado ko burgewa. Wani har ya jima da wayar tasa baya iya sanin wata bukata ta musamman da wayar za ta iya yi masa a al’amuransa na yau da kullum. Waya ta shafi dukkan wani bangare na rayuwar dan’adam har da tsaron rayuka da gujewa fadawa hadari kamar na masu yin garkuwa da mutane. Da yawan mutane suna amfani da manhaja na wayoyinsu, amma ba su gama kewayewa da abubuwan da wannan manhajan za ta amfane su ba.

Wani zai iya tambayar kan sa ta ya ya zan iya maganin garkuwa da mutane ko satar mutane ta hanyar amfani da wayar hannu? Wannan abu ne mai sauki kuma mai saukin ganewa. A yanzu mafi yawan masu amfani da wayoyi suna shiga dandalin sada zumunta na watsapp. Ta hanyar amfani da watsapp za ka iya maganin garkuwa da mutane, ko da an yi garkuwa da kai, to za a iya gane a inda kake cikin sauki. Yadda za ka yi hakan shi ne:
1. Ka kunna “location” na wayar ka.
2. Ka shiga watsapp sai ka zabi wanda kake so ka raba location din.
3. A kasa inda kake raba hotuna, za ka ga an baka zabi na “location” sai ka shiga za ka ga yana nuna maka inda za ka shiga a wannan lokacin. Bayan ya gama zai nuna maka unguwar da kake a taswira (map).
Daga nan kana da zabi guda biyu. Za ka iya turawa zuwa sabon waje da kake ko kuma ka tura rabawa zuwa wani wajen. Banbancin na farko da na biyun shi ne:
Turawa zuwa sabon waje shi ne, ka tura wa wani inda kake a wannan lokaci. Wannan zai taimaka idan aka kama mutum ba a san inda yake ba. Idan ya tura wa wani za a gane wajen da yake ba tare da shan wahala ba.
Duk wanda ka tura wa wannan wajen zai rika ganin duk inda kake a map din. Misali ka taho daga Kano, sai ka yi wa wani ‘sharing libe location dinka a Kaduna’, duk inda kake yana gani a nasa map din kuma yana nuna inda kake. Wannan zai taimaka shi ma wajen gane inda mutum yake. Zai fi taimaka wa jami’an tsaro wajen sanin matakin da za su dauka. Amma kai za ka fara taimaka wa kan ka duk sanda za ka yi tafiya mai tsayi, ka yi sharing ‘libe location’ dinka da wani a wani garin don gudun faruwar wani abu mai kama da garkuwa da mutane.

Ina fatan mutanen mu za su fara amfani da wannan dabara. Shi watsapp ba wai iya hirar chatting kawai ake ba har da irin wadannan muhimman al’amura wadanda suke taimaka wa tsaron rayuwa da dukiyoyin al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!