Connect with us

WASIKU

‘Jan Aikin Da Ke Gaban Atiku’

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Burin Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP wacce ta tsaida shi a matsayin gwaninta a zaben shugaban kasa nan da watanni kadan, shi dai babban burinsa ya kada shugaba Muhammadu Buhari. Wannan ba karamin buri bane, sannan ba karamin jidali bane. Atiku yana son karbar mulki ne a hannun wanda ya shekara 12 da shi da mutanensa suna rigimar su kai wannan matsayi. Idan zaben 2019 ya zo, a yankin kudu ne za a yi kare-jini biri-jini. Karfin PDP yana kudu, domin a arewa gwamna biyu rak take da su a kananan jihohi ta fuskar kuri’a wato da jihar Gombe da Taraba, sai gwamnoni biyu masu kome, Aminu Tambuwal na Sakkwato da takwarorinsa na Benue da Kwara.
Kalubalen PDP a yankin Yarbawa shi ne basu da gwamna ko daya. Sannan kuma cikin jihohi shidan, babu ko jiha daya da ba a rigimar shugabanci, a jiha uku ma da Ogun da Oyo da Ondo ‘yan takara bibbiyu PDP take da su a mukamin gwamna. A taron da aka yi a cikin satin nan a Ibadan don kaddamar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa, babu ko tawagar mutum guda daga jihar Osun. Haka kuma Yarbawa sun raina mukamin Sakataren gwamnati da Atiku ya yi musu alkawari in ya ci, ga shi kuma an karbe matsayin darakta janar na kamfen din Atiku daga hannun Olubenga Daniel na kasa, an rage masa karfi zuwa na shiyyar kudu.
A gefe guda kuma ita APC tana da gwamnoni shida, kuma duka gwamnonin suna kimanta Farfesa Yemi Osibanjo, wanda yake rike da mafi girman mukami da ya fito daga yankin, ministoci shida na yankin basa jayayya da juna, manyan ‘yan siyasar APC na yankin a kan takarar shugaban kasa basu da zabi sai Buhari.
Kalubale na biyu shi ne, a yankin Inyamurai. Ita PDP tana da gwamna uku, ita kuma APC daya, APGA guda daya.Cikin gwamnonin PDP Dabid Umahi na Ebonyi shi ne wakilin Atiku, ko sau daya bai je taron Atiku ba da aka yi a Ibadan da Ilorin da Sakkawato da shi da takwarorinsa na Enugu da Abia ko a wajen taron murnar zagayowar ranar haifuwar Atiku wanda aka kasaitaccen taro kuma aka gayyace su, ba a gansu ba. Gwamnan Anambra Willy Obiano na APGA ya bada sanarwa Buhari zai yi, babu ruwansa da tsohon maigidansa Peter Obi wanda yake marawa Atiku baya. Oshiomhole ya bata wa Rochas Okorocha, amma a matsayinsa na gwamnan Imo ya ce Buhari za su bi. Da Imo da Anambra su ne jihohin Inyamurai da suka fi yawan masu kada kuri’a.
Maganar gaskiya ma Sanata Ike Ekweremadu, wanda shi ne mafi girman mai mukami daga yankin Inyamurai daga PDP zuciyarsa da ta gwamnonin can guda uku tana rawa. Suna da korafi a kan salon da Atiku ya bi wajen zaben dan APGA a matsayin wanda zai rufa masa baya. Wasu bayanan ma sun ce su gwamnonin sun gwammance PMB ya taimakesu su zarce, shima su taimake shi ya zarce, in ya samu nasara ya zarce a basu shugaban majalisar dattijai, mataimakin shugaban kasa a kai kasuwa.
Idan kuma ka duba yankin Neja Delta, jihohinsu guda shida, jiha daya ce tak ta Edo ta APC. Sauran jihohin suna PDP. Su ne ke rike da dawainiyar jam’iyya, jihohinsu su suka fi kudi, don suna samun rarar man fetur, amma sun kyale Atiku shi kadai yake yin sabgarsa. Hasali ma gwamnan jihar Ribers Nyesom Wike, wanda shi ne maigidan shugaban jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus ya ajiye mukaminsa na kodinetan Atiku na yankin, yana neman hanyar da zai yi aiki da Buhari. Tunanin ‘yan Neja Delta shi ne gara su taimaka APC ta zarce, ala basshi a 2023 za su iya neman takarar shugabancin kasa a PDP. A ganin wasu ‘yan siyasarsu cin zaben PDP a 2019 komawa suka yi baya sosai a lissafin karba-karba na mulki a tsakanin Kudu da Arewa.
Nan Arewa kalubalen da Atiku yake fuskanta shi ne, akasarin wadanda suka bi tafiyarsa suna jira su karba daga gare shi, su kai ga biyan bukatunsu. Atiku ya fito ne gurin mutane da ‘yan siyasa a baba mai dala, ga shi kuma faduwa ta zo dai-dai da zama, ana yunwa da fatara da jahilci sosai a Arewa fiye da jihohin yankin kudu. Dadi da kari jiha daya ce rak a yankin da Buhari ya fito ake da gwamnatin PDP. Ma’ana yana da karancin mataimaka. Sauran jihohin na Buhari ne.
Duk da cewa kowane yanki uku na Arewa North West akwai tashin hankali da matsalar tsaro a Zamfara da Kaduna, akwai rikici a Adamawa da Taraba da Yobe da Borno a jihohin North East, akwai tashin hankali a Benue da Kogi da Nassarawa da Plateau a North Central, kaifin soyayyar Buhari ya dakushe sosai da sosai, ita kuma darajar Atiku ta karu, amma ma’aikatan da za su yi wa Atiku aiki su kuma barci suke yi, wadanda suka farka kuma suna jiran saukar daloli na kayan aiki. Shi kuma na Buhari suna nan da zafi-zafinsu.
In dai Atiku ya samu dama cikin kwana 40 masu zuwa ya warware wadannan matsalolin ya dinke baraka, ba shakka zai tabuka wani abu. In kuma an kasa ko suka yi tsamari har suka faskara, aka gagara cimma su, to a kwana da sanin za a kwana a ciki.
Sako daga Muttaka Ahmad, Sakkwato.
07034327715

•‘Ba Za Mu Taba Samun Gyara Ba A Nijeriya Har Sai…’
Salam, LEADERSHIP A YAU JUMA’A, don Allah ku bani dama in fadi irin nawa ra’ayin ga mutanan Nijeriya. Ina kira ga ‘yan Nijeriya su watsar da siyasar jagaliyanci sannan su rungumi siyasa haikan dan ci gaban al’ummarsu ba wai dan kansu ba kawai. Akwai abun tausayi da takaici irin yadda talaka suke shan bakar wahala a kasa me arziki irin NIjeriya. Adai-dai lokacin da talaka ya gane amfanin ilimi sai gashi sama da kaso goma na ‘ya’yansu zuwa makaranta ya gagare su saboda tsadar rayuwa. Kasa kamar NIjeriya, kamata ya yi a ce ilimin sakandire kyauta ne kuma dole ne kowanna yaro sai ya mallaki kwalin sakandire. A bayyane yake cewa shuwagabannin Nijeriya yawancin su maha’inta ne, babu abun suka yi wa kasa sai cin amanar talakawansu. kusan kullun halayen ‘yan Nijeriya kara baci yake yi sakamakon halin da aka jefa su. Dubun nan ma’aikatan da a da ba su san meye cin hanci ba, a yau wahala ta sa suna karba suna bayarwa. A yau wanda zai karbi cin hanci gare ka dan wata bukatar ka hakan ya zama taimako. Babu wata ma’aikata a Nijeriya da take yin aikinta na dai-dai. Ya Allah dan matsayin fiyayayyen halitta S.A.W ka tai maki shuwagabannin kasarmu Nijeriya, ka shirya mana zukatansu.
Sako daga Muhammad Idris, Kano.
07065279510

………..

Yana Da Kyau ‘Yan Siyasa Su Dinga Hada Kai
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya. Daga cikin matsalar da take damun kasar nan tamu a rayuwar zamantakewa, shi ne rashin hakuri da juna da kasa aiki tare da gaza amincewa juna cewa kowa da ranarsa. Muna da dabi’ar rigima da junanmu da gallazawa da raina fahimta da kuma tunanin kowa sai dai na shi. Wannan yana daga cikin sababin da yake jawo husuma da tarzoma har ta kai ga zub da jini da rasa dukiya da tsananin gaba a kasar nan, sakamakon yashin hadin kai ‘yan siyasa.
‘Yan siyasa ne kawai za ka ga suna aiki tare ba kyankyamin juna, babu gaba, za su daure su yi mu’amala da kowa, kuma kowa a bashi damarsa da ‘yancinsa, ‘yan siyasa suna son farantawa kowa, sannan suna son su tafi da kowa. Yaushe zamu samu irin wannan fahimtar a tsakanin kungiyoyin addini da kabilu da jama’ar yankuna a kasar nan? Yaushe zamu rika kokarin farantawa junanmu ba tare da nuna kowane irin banbamci ba?
Da zamu fahimci irin wannan siyasa a cikin kasar nan da mun ci gaba fiye da tutanin mu. in azan hankalin ‘yan siyasan kasar nan su rungumi a kidar hadin kai da juna.
Sako daga Isa Muhammed Gadanga, Abuja.
08039333264
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!