Connect with us

FILIN FATAWA

Yadda Ake Yin Sallah A Jirgin Sama Da Motar Haya

Published

on

Assalamu alaikum. Gafarta Malam ya halatta yin Sallar Farilla a cikin Mota/jirgin Sama da na Ruwa? domin wasu lokutan Mutum yakan yi tafiya mai nisa zuwa jihohin kudu ga lokacin Sallah ya yi ba sa tsayawa domin a yi Sallah, saboda mafi akasarin fasinjojin Ba Musulmai ba ne, kai har direban ma ba Musulmi ba ne.
Wa’alaikum assalam, to dan’uwa ya halatta ka yi sallah a jirgi ko mota, idan ya zama ba za ka sauka ba, sai bayan lokacinta ya fita, saboda fadin Allah madaukaki “Kuma Allah ya wajabtawa muminai sallah a cikin lokuta kayyadaddu” Surattunnisa’i aya ta:103.
Amma mutukar zaka iya riskar lokacinta bayan ka sauka, to ka jinkita ta daga farkon lokacinta, shi ya fi, saboda ka samu damar cika ruku’u da sujjada yadda ya kamata, hakanan idan tana daga cikin sallolin da matafiyi zai iya hada ta da ‘yar’uwarta, kamar azahar da la’asar, ko magriba da Isha, saboda za ka iya jinkirta ta farkon, ka yi ta hade da ta karshen.
Duk sallar da ka ji tsoron fitar lokacinta za ka iya yinta a jirgi ko mota gwargwadon yadda ka samu iko, don haka ya halatta ka yi nuni da ruku’u ko sujjada lokacin da kake sallah a mota, idan kuma jirgi ne mutukar ka samu damar yi a tsaye ba za ka zauna ba, sannan ka yi kokari a duka wajan fuskantar alkibla, sai in ya ta’azzara.
Annabi (SAW) ya halatta yin sallah a jirgin ruwa kamar yadda Albani ya inganta hadisin a Sahihul-jami’i a hadisi mai lamba ta: 3777, wannan sai ya nuna halaccin yi a mota da jirgin sama, saboda dukkansu ababen hawa ne.
Allah ne mafi sani

Idan Mutum Ba Shi Da ‘Ya’ya, Zai Iya Wasiyya Da Dukkan Dukiyarsa?

Assalamu Alaikum. Da Allah malam Inada tambaya kamar haka: Shin saurayin da bai yi aure ba amma yana da iyaye da ‘yan’uwa a raye, zai iya yin wasiya da rabin dukiyarshi kasancewar bashi da ‘ya’ya? Na gode
A zahirin hadisai ingantattu har wanda ba shi da ‘ya’ya ba zai yi wasici da sama da daya daga cikin uku na dukiyarsa ba, saboda Annabi s.a.w yana cewa da Sahabinsa Sa’ad (RA) lokacin da ya so ya yi wasiyya da mafi yawan dukiyarsa: “Ka bar magadanka cikin wadata, ya fi ka bar su matalauta suna rokon mutane”.
Kasancewar Annabi (SAW) ya yi amfani da lafazin magada, hakan sai ya nuna ko ba ‘ya’ya ba za’a yi wasiyya da sama da daya cikin uku na dukiya ba, saboda hakan zai cutar da ragowar magada, ya iya jefa su cikin talauci bayan mutuwar magajinsu.
Aya ta: 12 a cikin suratu Annisa’i tana nuna cewa: Wanda zai mutu ba shi da ‘ya’ya, ba shi da iyaye, ba zai yi wasiyya da abin da zai cuci magadansa ba.
Allah ne mafi sani.
Zan Iya Rike Hannun Budurwata?

Malam Ya Hukunchin Wanda ya rike Hannun wata mace Kuma ba matarsa ba ce, amma Budurwarsa ce?
Wa’alaikumus salam, Bai hallata mutum ya rike hannun wacce ba muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance ba ya Musafaha (hada hannu) da mata yayin da zai musu mubaya’a, yana yi musu mubaya’a ne da Magana, kamar yadda ya tabbata a hadisi.
Taba hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga Zina saboda yana tayar da sha’awa, Allah Madaukaki ya haramta kusantar zina a aya ta 32 a suratul Isra’i, Zina tana daga cikin manyan zunuban da babu kamar su bayan shirka da Allah. Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai kiyaye shi, wanda ya bı son zuciyarsa, to Allah yana nan a madakata.
Allah ne mafi sani.

Mace Za Ta Iya Zama Alkali A Musulunci?
Assalamun alaykum Warahmatullahi wabarakatuhu. Bayan sallama irin ta musulunci malam inayi maka fatan alheri Allah yasa kana cikin koshin lafiya. Tanbayata malam ya halatta mace ta yi alkalanci a musulunci. Allah yakarawa malam lafiya.
Wa’alaikum assalam, a wajan mafi yawan malamai mace bai halatta ta yi alkalanci ba, saboda hadisin Abu-bakrata wanda Annabi (SAW) yake cewa: “Duk mutanen da suka jibintawa mace lamuransu ba za su rabauta ba. Alkalanci yana bukatar nutsuwa da daidaiton yanayi, wannan yasa Annabi (SAW) ya hana wanda yake cikin fushi ya yi alkalanci, kamar yadda Bukhari ya rawaito, mace kuma idan ta fara jinin haila takan fita daga daidaito, wannan yake nuna rashin dacewarta da wannan aiki na Annabawa da manzanni.
Allah ne mafi sani.

Yaushe Ya Dace Na Fara Saduwa Da Amaryar Da Na Aura Tana Karama?
Assalamu alaikum. Ina fatan Allah ya kara ma malam Ikhlasi. Ya halatta idan mutum ya auri mace karama wadda ba ta fara jini ba ya sadu da ita? Ko kuwa rainonta zai yi?
Wa’alaikum assalam, Malamai sun cimma daidaito game da halaccin aurar ‘yar karamar yarinya, saboda aya ta hudu a suratu Addalak ta bada labarin yadda karamar yarınya za ta yi idda, hakan sai ya nuna ingancin yi mata aure kafin ta balaga, sannan Annabi (SAW) ya auri nana Aisha tana ‘yar shekara shida.
Malamai sun yi sabani game da lokacin da za’a fara saduwa da ita, bayan an yi auren, akwai wadanda suka tafi akan cewa dole sai ta balaga za’a mikata ga mijinta. Wasu malaman sun kayyade shi da shekara (9) saboda Annabi (SAW) ya tare da nana A’isha ne bayan ta kai shekaru tara.
Zancen da ya fi zama daidai shi ne: za’a duba yanayin jikin yarinyar, in har za’a iya jima’i da ita ba ta cutu ba, za’a iya mikata ga mijinta, ko da shekarunta kadan ne, saboda mata suna bambanta wajan girman jiki gwargwadon wurin da suke rayuwa, da kuma irin abincin da suke ci, sannan sharia ba ta iyakance lokacin da ake fara jima’i da mace ba.
Don neman karin bayani duba: Al-Mugni 27/77 da kuma Alminhaj na Nawawy 9/206.
Allah ne mafi sani

Yaya Alamomin Balagar Namiji Suke?
Assalamu alaikum, Allah ya Ya saka ma Dr da alkhairi, ina da yaro ne mai kimanin shekara goma sha uku (13) yana da girman jiki don ya fi ni tsawo na dauka girman a tsayi ne kawai sai larurar basir ta same shi na zo in yi masa tsomen magani sai mamaki ya kamani yaron halittarsa kamar na magidanci na yi wa mahaifinsa bayani ya ce in tambaye shi yana mafarki na tambaye shi ya ce ba ya yi. Tambayata a nan shi ne hukunchin baligi ya hau kansa ko kuwa?.
Wa’alaikumus salaam, alamomin balagar namiji guda uku ne:
1. Yin mafarki, kamar yadda aya ta: 59 a suratu Annur ta tabbatar da hakan.
2. Tsirowar gashin mara, kamar yadda kissar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Banu-Kutaitha ta nuna hakan na daga cikin alamomin girma.
3. Cika shekaru (15), kamar yadda Malamai suka fahimci haka a hadisin Ibnu-Umar lokacin da za’a fita yakin Uhudu.
Duk alamar da ta fara zuwa ma Da namiji daga çıkın alamomi ukun da suka gabata, to ya zama baligi kuma shari’a ta hau kansa, ba shi daga çıkın alamomin balaga girman mazakuta, zai yı kyau ki sake tuntubar yaronki don tabbatar da daya daga cikin abin da ya gabata.
Allah ne mafi sani.

Mace Za Ta Iya Yin Aure Ranar Da Ta Gama Takaba?
Assalamualaikum malam meye matsayin auren da aka daura randa mace tagama takaba?
Wa’alaikum assalam, in har kwanakin iddar sun cika auran ya yi, saidai Allah ya haramta neman aure cikin idda, in har ya zama an fara neman auran ne tun kafin ta kammala takaba, to tabbas an sabawa aya ta (235) a suratul Bakara, saba dokar Allah yana jawo matsaloli.
Allah ne mafi sani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!