Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Yadda Allah Yake Magana Da Annabi (SAW) Cikin Tausasawa (2)

Published

on

Malam Alkadiy Iyad ya ce idan aka dubi wannan ayar, ya wajaba ga Musulmin da yake tarbiyyantar da zuciyarsa da ragamar Shari’a (tun ma ba wanda ya ce shi malami ne ba) ya rika ladabtuwa da ladabin Alkur’ani. Ma’ana kar ya dinga yin hukunci da fadar abin da ya ga dama, ya dinga lura da yadda Alkur’ani yake fadar magana musamman ma idan maganar ta shafi Annabi (SAW) da sauran Sahhabansa masu girma har zuwa kan malaman al’umma. Idan magana ta zo, kar mutum ya dinka kwakule-kwakule a ciki wai don shi yana so sai ya tona komai. Da yawa wasu daga cikin mutane idan ba su ji abu daga bakin malami ba babu ruwansu da shi amma idan suka ji a wurinsa shikenan, walau sun gane ko basu gane ba kawai za su yi amfani da fahimtarsu wurin yiwa abin hukunci bisa kafa hujjar cewa malami ne ya fadi abin. Idan laifi ne ko kuskure ka ga an dora al’umma kan wata turba da ba ta dace ba.

Alkur’ani yana da alkunya, misali; a kan maganar saduwa da mace sai ya sakaya abin ya ce “shafar mace”, malamai idan suka zo fassara sai su yi bayani cikin hikima a kan saduwa. Idan wurin lalata da maza ne ma Alkur’ani sai ya sakaya ya ce “wadanda ke zuwa wa maza maimakon mata”, bai fito da abin karara ba saboda koyar da mu dattaku. Bai kamata a yi ta warware magana babu ladabin Shari’a da koyi da ladabin Alkur’ani ba. Idan kana karatu sai ka zo wurin da aka taba manya, to ko ka ga laifin da aka ce an yi; ka yi kokarin yi masa mafita; idan ba za ka iya ba ka kame bakinka in ko ba haka ba a maimakon gyara sai mutum ya yi barna. Fir’auna kafirin da ya ce shi Allah ne, Allah ya umurci a fada masa magana mai dadi a cikin Alkur’ani. Allah ya ce wa Annabi Musa (AS) da Annabi Haruna (AS) su fada wa Fir’auna magana mai dadi ko zai wa’azantu. To ina ga wanda laifinsa ko rabin na Fir’auna bai kai ba fa? Rashin bin ladabin Alkur’ani duk ya ja mana shiga cikin halin da muka fada yau. Mutum don ya ce shi Musulmi ne ko malami ko almajiri, sai ya rika fadin abin da ya ga dama a matsayin addini ko ya yi hukunci yadda ya ga dama ga kowa, abin har ya wuce maganar baki ya kai ga daukar makami ana kashe jama’a. Duk rashin bin ladabin Alkur’ani ya kawo mana haka. Ba mu gyara bakinmu ba kuma idan baki bai gyaru ba zuciya ba za ta gyaru ba. Mu yi kokarin bin ladabin Alkur’ani cikin maganganunmu, da gogayyarmu, da ba da amsoshin tambayoyi a cikin karatuttukanmu.

Alkur’ani shi ne kololuwar sannai (jam’in sani), shi ne dausayin ladabai na addini da na duniya baki daya. Musulmi ya dinga kula da wannan tausasawa mai ban mamaki cikin tambayar da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) a wannan ayar ta “Allah ya yafe ma, me ya sa ka yi musu izini, (Ma’ana Allah zai tambayi Manzon Allah (SAW) ne amma sai da ya hada tambayar da afuwa). Lallai mutum ya rika lura da fa’idodin ladabi da ke cikin ayar. A lura cewa, Allah (SWT) sai da ya fara da afuwa kafin tambayar ta rarauka. Kuma koda ma wadanda suke ganin Annabi (SAW) laifi ya yi Allah yake masa ‘fada’ a cikin ayar, to ai Allah ya ce ya yafe kuma yafiyar aka fara ambata kafin rarauka din. Wannan yana kara tabbatar da cewa babu wani laifi a cikin izinin da ya bayar (SAW). Allah ya kara amintar da zuciyar Annabi (SAW) daga tsoron a ce masa ya yi laifi kafin a tambaye shi cewa “me ya sa ya yi musu izini?”.

A cikin wata ayar Allah (SWT) yana cewa “ba domin mun tabbatar da kai ba (ya Rasulallah) ka kusa karkata kadan zuwa gare su”. Wani sashe na malaman Tafsiri sun ce Allah ya yi wa Annabawa (Alaihimus salam) rarauka da yawa, amma sai bayan da suka yi tuntube da abin da suka yi sannan Allah ya yi musu raraukar. Amma shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) ta bangarensa, rigakafin ya ji a ransa cewa ya yi laifi Allah ya yi masa. Manzon Allah shi ne mafi kiyaye dokokin Allah da soyayyarsa saboda Allah ya ce “ba domin mun tabbatar da kai ba ka kusa ka karkata kadan zuwa gare su”. Wannan yana nuna Allah ne da kansa ya jibinci lamarin tabbatar da kiyaye Manzon Allah (SAW) daga barin aikata abin da za a yi masa rarauka a kai. A cikin rashin tsoratar da shi sai Allah ya kubutar da shi. Misalin yadda za a fahimci haka shi ne, wani dan kasuwa ne ya koya wa wani mutum kasuwanci, bayan dan wani lokaci sun zo suna hira sai wannan dan kasuwan ya ce wa mutumin “ba domin na koyar da kai kasuwancin nan ba; da ka zubar da jarin da na baka”. Ma’anar wannan maganar tana nufin salwantar da jarin nan abin tsoro ne kuma hakan ba ta auku ba bisa dalilin koyar da wannan mutumin kasuwancin da yake yi.

To Allah ya kiyaye Manzon Allah (SAW) ga barin karkata zuwa ga mutanen nan kasancewar shi da kansa (SWT) ya tabbatar da shi ta yadda ba zai yi hakan ba. A cikin bashi tsoro (na barin tarku aula) sai Allah ya girmama shi tare da darajanta shi.

Yana daga irin wannan magana fadin Allah cewa “Hakika mun sani abin da kafiran nan suke fada maka yana bata maka rai, sai dai ba su danganta ka da karya (ko ba sa karyata ka, a wata kira’ar) sai dai azzaluman nan (kafirai) suna jayayya ne da ayayoyin Allah”. Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu) ya ce sanadin saukar wannan ayar shi ne: Abu Jahli ne ya ce wa Annabi (SAW) “Muhammadu; mu fa ba ma karyata ka, mun san kai maigaskiya ne, abin da ka zo da shi ne ba mu yarda da shi ba muke karyatawa.” An ruwaito cewa a yayin da mutanen Annabi (SAW) suka karyata shi sai Annabi ya yi bakin ciki, sai Jibrilu (AS) ya zo masa ya ce “me ya ke bata maka rai (ya Rasulallah)?”, sai Annabi (SAW) ya ce “mutanena ne suka karyata ni”, sai Jibrilu ya ce masa “mutanenka sun san kai mai gaskiya ne, ba da kai suke ba; da ayar Allah suke”, daga nan sai Allah ya saukar da wannan ayar.

A cikin ayar akwai macira mai saukin riko cikin baiwa Manzon Allah hakuri da shafar zuciyarsa cikin lallashi cewa Allah ya tabbatar Manzon Allah maigaskiya ne, haka nan ma a wurin kafiran domin da kansu sun furta cewa shi (SAW) maigaskiya ne tare da kudurce hakan har ya zamo suna kiran sa da sunan Aminu (Amintacce) tun kafin Annabta. Allah ya dauke wa Manzon Allah (SAW) damuwar zuciyarsa ta hanyar tabbatar da cewa hatta su kansu kafiran sun san shi (SAW) maigaskiya ne. Kuma sai Allah ya sanya zargin (karyar) ga kafiran ta hanyar ambatar su da sunan masu jayayya da ayoyinsa kuma azzalumai.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!