Connect with us

LABARAI

An Samu Karuwar Hasken Lantarki Zuwa Migawat 116,659.8 A Watan Nuwamba

Published

on

Kamfanin samar da hasken lantarki na kasa, ya bayar da hasken lantarkin da ya kai karfin megawatt 116,659.8, a watan Nuwamba, saboda karuwar hasken lantarkin da aka samu.

Lissafin karfin hasken lantarkin da aka samu daga kamfanin na TCN, ya yi nuni da cewa, daga ranar 2 ga watan Nuwamba zuwa 30 ga watan na Nuwamba, an samu hasken lantarkin da ya kai karfin 116,659.8 mw.

A bisa sabanin 107, 864.8 mw da aka samu a watan Oktoba.

Hakan ya nuna an sami karin hasken lantarkin da 8,795 mw kenan a tsakanin watan na Oktoba da Nuwamba.

An bayar da rahoton da ke nuni da cewa, daga ranar 1 ga watan na Nuwamba zuwa 15 ga watan na Nuwamba, an sami 3,681.7mw, 3,776.1mw, 3,703mw, 3652.5mw, 3,810.5mw, 4,204mw, 3,913.6mw, 3,762mw and 3,712.6mw.

Sauran su ne: 3,493.6mw, 3,903.50mw, 4,998.8mw, 4,229.7mw and 4271.8mw.

Wannan ya nuna cewa, a kullum ana samar da hasken lantarkin daga 16 ga watan na Nuwamba zuwa 30: 4,168.2 mw, 4,125.5mw, 3,891.5mw, 4,067.5mw, 3,880mw, 4,523.4mw, 4,302mw da 4,089.2mw.

Sauran su ne: 3,883.6mw, 3,846.5mw, 4,137.7mw, 4,229.3mw, 4,043.8mw, 4,141.6mw da 4,216mw.

Ana raba hasken lantarkin ne zuwa tashoshi 11 masu raba hasken lantarkin.

Kamfanin samar da hasken lantarkin yace, har yanzun dai abin da kasar nan ke bukata na hasken lantarkin shi ne, 19,100.00mw, amma a halin yanzun ana iya samar da 11,165.40mw.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!