Connect with us

RAHOTANNI

Burutai Ya Yi Kira Ga Sojoji Su Kawo Karshen Kashe-Kashe A Zamfara

Published

on

Shugaban rundunar sojojin Nijeriya Lt Janaral Tukur Burutai ya yi kira ga rundunar sojoji da ke Gusau jihar Zambara, su kora kokari wajen yaki da ‘yan ta’adda da ke cikin jihar. Burutai ya yi wannan kira ne ga kwamantar rundunar Manjo-Janaral Hakeem O. Otiki a shalkwatan rundunar da ke Gusau cikin babban birnin jiahar Zamfara. Ya bayyana cewa, hallarar rundunar a cikin jihar zai sa yakin da ake yi da ‘yan bindigan ya kara tsananta. A cewarsa, matakin kara maida rundunar jihar Zamfara zai karfafa tsaron mutanen jihar daga farmakin ‘yan bindiga. Ya kara da cewa, rundunar tayi kokari wajen kawo karshan kashe-kashen ‘yan bindiga cikin jihar, ya kuma bayyana cewa, rundunar za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro dan yaki da ayyukan ‘yan ta’addan jihar.

A jawabinsa, kwamandar runduna ta takwas da ke jihar Sakkwato Manjo Janaral Stebenson Olabanji ya bayyana cewa, maido da rundunar jihar Zamfara ya biyo bayan matsalar tsaro da jihar take fuskanta. Kwamandan wanda aka kara nada shi a matsayin kwamandan da ake kika sasuna Sharan Daji, ya kara da cewa, rundunar sojojin za ta kara wa ayyukan rundunar Sharan Daji.

Sakataran gwamnatin jihar Farfesa Abdullahi Shinkafi wanda ya wakilci gwamna Abdul-Aziz Yari, ya yi maraba da sake dawowa da rundunar cikin jihar. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta baiwa rundunar da sauran hokumomin tsaro da ke jihar duk wata gudummawan da suke bukata domin yakar ‘yan bindigan.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!