Connect with us

RAHOTANNI

Duniya Na Fuskantar Barazar Labaran karya –Fatima Shu’aibu

Published

on

An bayyana cewa ba Nijeriya ce kadai ke funskantar barazanar labaran karya ba, matsala ce da ta shafi duniya gaba daya. Wata Malam a fannin koyar da aikin jarida a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, Malama Fatima Shu’aibu ta bayyana haka a takardar da ta gabatar a wajen taron shekara-shekara da Matatar mai ta Kaduna (KRPC) ke shiryawa manema labarai a Kano.
Malamar wadda ta bayyana illolin da labaran karya ke yi wa al’umma da kuma yadda kafafen watsa labarai da aka sansu da gaskiya suke kokarin bata sunan su ta hanyar ba da labaran da ba na gaskiya ba.
Ta ce akwai wasu manyan kafafen yada labarai a Nijeriya, wanda a kwanakin nan aka kai su kotu saboda sun bayar da labaran karya. Hakan ta sanya dole suka ba da hakuri. Ta ce wannan na yi wa kafar sadauwa illa, matukar tana ba da labaran karya ko ta ba da labarin gaskiya ba za a yarda da ita ba.
Malama Fatima Shu’aibu ta kuma bayyana cewa akwai matsaloli sosai ga kafafen yada labarai musamman wadanda suke ta kafofin sadarwa. Ta ce idan ka karanta labarin da wata kafar ta rubuta za ka ji kamar ka yi kuka saboda rashin iya rubutu. Don haka ta bayyana cewa dole sai an dage za a iya kawar da wannan matsala a duniya. Dole ne ‘yan su rinka samun horo akai-akai don inganta ayyukansu.
Ta ce dole ne mu zama masu daukar nauyin abin da muka rubuta, dole ne mu dauki nauyin abin da muka watsa ws duniya.
Ta kuma ba da misali da yadda kafofin yada labarai suka ba da rahoto lokacin zaben shekarar 2015. Ta ce kusan dukkan kafafen yada labarai suna ba da labarin da ya sha banban da ba juna. Ta ce idan kana kallon NTA ne za ka ga Jonathan ne ke kan gaba. Idan kuma kana kallon TbC ne za ka ga Buhari ne ke kan gaba. Ta ce wannan kuma ya samo asali ne kan masu tallafa wa ita kafar yada labarai din ne. Ko dai wanda suke goyon baya yana ba su kudi ko kuma wani abu ba daban.
Daga karshe ta kuma bayyana hanyoyin da ya kamata a bi don gane labaran karya. Ta ce za a iya gane wannan ta hanyoyi da daman gaske. Duba ga kwanan wata da aka sanya labari. Hoton da ke kan labari zai iya tabbatar maka da cewa labarin gaskiya ne ko na karya.
Da yake tsokaci kan wannan takarda, Babban daraktan gudanarwa na Matatar Mai ta Kaduna, Dakta Abdullahi Idris, ya bayyana godiyarsa ga Malama Fatima, ya ce ta ba da gudunmawa yadda ya kamata sosai.
Shi kuwa Malam Abubakar Jidda Usman, ya bayyana cewa akwai bukatar a yi yadda ya kamata don magance wannan matsala. Ya ce ba zai iya tuna lokacin da aka baiwa dan jarida ministan yada labarai ba a Nijeriya. Ya ce an bar jaki ne ana dukan taiki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!