Connect with us

MANYAN LABARAI

Labarin Kanzon Kurege: Yadda Ya Hargitsa Kaduna Kwanan Baya  – el-Rufa’i

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i ya nemi sassan majalisa da shari’a na jihohi su fito da doka mai tsauri da za ta dakile baza labaran kanzon kurege da kalamai na haddasa husuma.

Gwamnan ya yi kiran ne a lokacin da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya kai ma sa ziyarar ban-girma, a wani bangare na taron koli na Majalisar Yada Labarai ta Kasa karo na 47 da ya gudana a babban birnin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya ya ruwaito cewa Ministan tare da kwamishinonin yada labarai na jihohi, da shugabannin hukumomin yada labarai na gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai suka halarta.

Babban taken taron shi ne, “Yaki da Labaran Karya da Kalaman Haddasa Husuma domin Karfafa Hadin Kan Kasa”.

Gwamna el-Rufa’i wanda ya ce taken taron ya dace sosai, ya kara da cewa Kaduna ta sha fama da matsalar kalaman tayar da husuma da yada labaran kanzon kurege fiye da duk wata jiha a fadin kasar nan. Ya nunar da cewa labaran kanzon kurege za su iya daidaita kasa, don haka akwai bukatar samar da dokoki masu tsauri a kai.

El-rufa’i ya kuma ce Kaduna kamar sauran jihohin Nijeriya sun samu koma-baya saboda amfani da tsofaffin dokoki da zamanin aiki da su ya wuce wurin yakar labaran kanzon kurege da kalaman tayar da husuma.

Musamman, Gwamnan ya jaddada cewa ya kamata a fadada ayyukan manyan kotuna na jihohi domin su samu dokokin hukunta laifin damfara ta intanet wanda zai ba da damar zakulo masu yada labaran kanzon kurege a kafafen sadarwa na walwalar jama’a. Inda ya kara da cewa jihohi ba za su iya hukunta masu aikata wadannan laifukan ba, saboda tsarin dokokin da suke amfani da shi.

Gwanan ya buga misali da wani labari na boge da wani mai suna Aminu Maikori ya yada a kafar sadarwa ta walwalar jama’a cewa Fulani Makiyaya sun yi kwantar-bauna tare da kashe mutum biyar a Kwalejin Ilimi na Gidan Waya da ke Kudancin Kaduna.

Ya ce labarin wanda ya zama na karya bayan bincike, ya haddasa hare-haren ramakon-gayya, “amma kuma wanda ya kirkiri labarin yana nan yana yawonsa a titi cikin takama saboda babu wata sahihiyar dokar hukunta shi

“Audu Maikori yana zaune cikin nishadi a gidansa da ke Legas ya ba da labarin cewa an kashe dalibai biyar masu nazarin aikin jarida a Kwalejin Ilimi na Gidan Waya wanda kwata-kwata karya ce tsagwaronta.

“Mun fara bin diddigin hukunta Audu Maikori kuma da ya gano cewa an-kai-shi-an-baro, sai ya janye labarin kuma ya dauka shi kenan abin ya tafi a banza. Amma mun ce a’a, sai mun ga an daure shi a gidan yari tukuna. To amma wannan tun a shekarar 2016 ne ya faru, yanzu kuma muna 2018 har yanzu a matsayin beli yake. Muna da manyan matsaloli. Muna bukatar a baiwa gwamnatocin jihohi da manyan kotunan jihohi hurumin yi wa irin wadannan mutanen shari’a saboda gwamnatin tarayya ba za ta iya ba ita kadai

“Abin da muke tunanin yi a Jihar Kaduna shi ne mu kafa dokokin da za su dakile wannan aika-aikar na kasahin kanmu. Muna bukatar kyakkyawan tsari da zai yi dai-dai da cigaban kimiyya da fasahar da ake da su yanzu”, in ji shi.

Gwamna el-Rufa’i bai tsaya a nan ba, har ila yau ya yi bayanin cewa an tayar da rikici a Kasuwar Magani da cikin garin Kaduna ne a kwanan baya sakamakon kalaman tayar da husuma.

“An fara yada jita-jitar cewa an kashe Sarkin Adara da aka sace ana garkuwa da shi kuma kafin kiftawa da bisimillah cikin sa’a daya tak an kashe mutum 22 a hare-haren ramakon-gayya.

“Labarin da aka yada (na karya) shi ne, wai na gayyaci Sarkin wani taro sai na fada ma sa cewa masarautarsa za a daga darajarta zuwa mai daraja ta daya, da ya nuna rashin yardarsa da hakan sai na ce zan yi maganinsa.

“Don haka, da aka sace shi a hanyarsa ta dawowa zuwa Kachia, sai aka ce ni na tsara yadda za a sace shi. Wannan shi ne musabbabin tashin rikicin kuma duk wannan labarin na karya ne.

“Ban taba gayyatar wani Sarki zuwa fadar gwamnatin jiha ba tare da sun rubuta neman haka daga gare ni ba saboda wani kwakkwaran dalili.

Gwamnan ya yi tambayar cewa, “Me ya sa zan yi sa-in-sa da Sarkin ko sace shi, alhali idan har ya taka doka ina da cikakken ikon da tsarin mulki ya ba ni na rushe masarautarsa.

“Abin bakin ciki, wannan ne labarin karya da aka yada, ya daga hankulan jama’a kuma har yanzu akwai wasu yankuna na masarautar da aka sa dokar hana fita na wani lokaci,” a ta bakinsa.

Gwamna el-Rufa’i ya yaba wa majalisar ta yada labarai bisa kawo taron nata Kaduna, kana ya hori mahalarta da su bayar da shawarwari masu karfi da za su magance baza labaran karya da kalaman tayar da husuma a cikin al’umma.

Tun da farko, Minista Lai Mohammaed ya yi kira ga jihohi su tallafa wa gwamnatin tarayya wajen yaki da labaran kanzon kurege da kalaman tayar da zaune tsaye.

Ya ce baza labarin kanzon kurege na faman karuwa kamar wutar daji saboda ‘yan adawa suna amfani da shi wurin batanci ga gwamnatin Buhari gabannin zabukan 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!