Connect with us

RAHOTANNI

Majalisar Dattawa Ta Amince A Kashe Dala Biliyan 1 Wajen Kammala Kamfanin Sarrafa Karafa Na Ajaokuta

Published

on

A jiya ne ‘yan majalisar dattijai ta amince wa gwamnatin tarayya ta kashe kudi dala biliyan 1 daga harajin da take samu na danyen man fetur, domin kammala aikin kamfanin sarrafa karafuna na Ajaokuta. Majalisar ta ce, ta amince wa gwamnati a kan duk wani kudin da za ta samu lokaci bayan lokaci ta kashe domin kammala aikin na wannan kamfani. Bugu da kari, za a hada da duk wani bashi ko kuma tallafi wanda wannan kasa da ta samu domin kammala aikin kamfanin sarrafa karafuna na Ajaokuta. Majalisar ta amince da wannan kudiri ne bayan wani zama da tayi mai taken “Ajaokuta Steel Company Completion Fund Bill, 2018” wanda shugaban majalisa da kuma sanata Ahmed Lawan suka gabatar.

A ranar 28 ga watan Maris, majalisar wakilai na tarayya ta amince da irin wannan kudiri domin a samar da kudade wajen kammala aikin kamfanin sarrafa karafuna na Ajaokuta. An duba wannan kudiri sannan kuma dukkan ‘yan kwamintin suka amince, inda suna bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta kammala shirin wannan aikin kamfani. Ita wannan duka ta bayyana cewa, duk wani kudi da minista zai kashe a kan gyara, inganta, fadadawa, canca kayayyakin more rayu, sayan kayayyakin aiki da kuma sauya dukiya da ake bukata wanda ya hada da kammala aikin kamfanin sarrafa karafuna na Ajaokuta to sai majalisa ta amince. “Duk wani kudi wanda za a sayi fili to san an bi ta hunnun wannan duka. Gudanar da duk wani bincike na musamman a kan wannan aiki yana sakin layi na (a) da na (b) ko kuma wani shiri na habaka ko na ci gaban kammala aikin kamfanin sarrafa karafuna na Ajaokuta”

Mataimakin shugaban majalisa sanata Ike Ekweremadu wanda shi ne yake jagorantar kwamitin ya bayyana cewa, idan aka rattabawa wannan kudiri hannun ya zama duka, zai sa a yi saurin kammala wannan aiki na kamfanin sarrafa karafuna ta Ajaokuta.

Har ila yau, ‘yan masalisar sun amince da shirin shugaban kasa na gyaran dokar shekarar 2018 na tarbiya (assasawa da kuma zantarwa). Dokar za ta assasa shirin fadar shugaban kasa ta yin afuwa ga mutanen yankin da suka kwance damarar yaki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!