Connect with us

RAHOTANNI

Mutum Hudu Sun Mutu A Arangama Da Masu Garkuwa

Published

on

A ranar Litinin ne mutum hudu suka rasa rayukansu a wani arangama tsakanin masu garkuwa da mutane da kuma mazauna kauyen Dalla Mahuta da ke karamar hukumar Dandume cikin jihar Katsina.  Bincike ya bayyana cewa, wadanda ake zargin masu satan shanu da kuma yin garkuwa da mutane su 20 ne suka mamaye kauyen da misalin karfe 1 na dare, inda suke ta harbi sama da bindigogi kirar AK47. An bayyana cewa, ‘yan bindigan sun yi kokarin yin garkuwa da wani mazaunin kauyen mai suna Alhaji Abdulrahman, sai suna harbi wani mutum mai suna Aminu Maharazu dan shekara 20.

Mazauna kauyen sun yi sauran daukar mataki, inda suka hada kansu suka duranma ‘yan bindigan, mutum uku daga cikin masu garkuwan sun rasa rayukansu, inda sauran suka guda zuwa cikin daji.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isah ya bayyana cewa, ‘yan sanda wadanda ke bakin aiki sun garzaya zuwa wajen da lamarin ya auku, sun samu mulmulen harsashi guda biyar da kuma bawon harsashin da aka harba guda uku. “An samu gawar daya daga cikin kasungumin shugaban masu garkuwa da mutane wanda mazauna kauyen suka kashe mai suna Isiya Alhaji Bello dan asalin kauyen Gamji da ke karamar hukumar Sabuwa cikin jihar Katsina, wanda ya fitini yankunan Dandume, Sabuwa da kuma Kankara,” inji shi.

Rundunar ‘yan sanda ta fasa gungun ‘yan fashi da makami wadanda suke yi wa mutane fashi a cikin jihar tare da kashe shugaban ‘yan bindigan. “Rundunar ‘yan sanda wadanda suke gudanar da aiki a kauyen Alhazawa cikin karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina sun bude wuta a kan masu satar shanu da kuma yin garkuwa da mutane, inda suka samu nasarar kashe shugaban su mai suna Audu Bello wanda aka fi sani da Gemu dan shekara 40 a dajin Rugu,” kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isa shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Katsina.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!