Connect with us

SIYASA

Jadawalin ’Yan Majalisar Tarayyar Da Ba Za Su Koma Kujerunsu Ba

Published

on

Dab da zuwan babban zaben 2019, akalla kashi 50 ne na ‘yan Majalisun tarayya ta 8, su 360, ba za su komo kan kujerun na su ba, a zaman Majalisar na 9, a  shekara mai zuwa.

Da yawan ‘yan Majalisun, ko dai sun fadi ne a zabukan fitar da gwani na Jam’iyyun su da aka kammala kwanan nan, ko kuma sun nemi wasu mukaman ne da ke saman wadanda suke a kai.

Jadawali na kasa, bayani ne na ‘yan Majalisar Wakilai da tabbas ba za su komo kan kujerun na su ba a 2019 sabili da dalilai daban-daban.

 

 • ABIA

A Jihar Abia, ‘yar majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta, Bende, Nnenna Elendu-Ukeje, ba za ta komo kan kujeran na ta ba, domin ta kasa samun tikitin Jam’iyyarta ta PDP a zaben fitar da gwani.

Ba kamar wasu takwarorin ta ba, ba ta nemi tsayawa ba kuma a wasu Jam’iyyun.

 

 • ADAMAWA

Uku daga cikin ‘yan Majalisan tarayya na Jihar ba za su komo bisa kujerun na su ba.

Daga cikin ukun, biyu sun gaza samun tikitin Jam’iyyar APC ne a zaben fitar da gwani, na ukun kuwa ya nemi kujerar dan Majalisar Dattijai ne, wanda kuma bai samu ba.

Sauran ‘yan Majalisun biyu da suka fadi a zaben na fitar da gwani su ne, Shuaibu Abdulrahman da Abubakar Lawal. Takwaran su, Adamu Kamale, ya nemi yin takaran Majalisar Dattawa ne, ya kuma fadi zaben.

 

 • AKWA IBOM

Biyu daga cikin 10 na ‘yan Majalisun tarayya daga Jihar Akwa Ibom, sun gaza samun tikitin Jam’iyyar a zaben fitar da gwani, don haka ba za su komo Majalisar ba.

Su ne kuwa, Samuel Ikon da Owoidighe Ekpoatai.

 

 • BAUCHI

Uku daga cikin ‘yan Majalisu 12 daga Jihar ta Bauci, ba za su dawo Majalisar ba, a karo na gaba.

Su ne, Shehu Aliyu, Haliru Jika da Adamu Gurai.

Sa’ilin da,  Messrs Aliyu da Gurai, suka fadi a zabukan fitar da gwani na Jam’iyyun su, Mista Jika, shi ya sami tikitin Jam’iyyar na shi ne na yin takaran kujerar Majalisar Dattawa. Ana sa ran zai gwabza da, Isa Missau.

 

 • BAYELSA

Dan Majalisar tarayya guda ne ba zai komo Majalisar ba daga Jihar ta Kudu maso Kudu, mai arzikin man fetur, domin bai haye a zaben fitar da gwani na Jam’iyyarsa ta PDP ba.

Shi ne kuwa, Sodagumo Omoni, mai wakiltar mazabar tarayya ta, Ogbia.

 

 • BENUE

Biyar daga cikin ‘yan Majalisun tarayya 11 daga Jihar  ta Benuwe, ba za su komo Majalisar ba a zaman Majalisar na gaba.

Su ne kuwa, Emmanuel Orker-Jeb, Dickson Tackighir, Saleh Hassan, Emmanuel Udende da Ezekiel Adaji.

Sa’ilin da, Mista Orker-Jeb, zai kada tutar Jam’iyyar PDP ne a mazabar dan Majalisar Dattawa, sauran duk sun gaza samun tikin Jam’iyyar ne a zabukan fitar da gwani a Jam’iyyun su.

 

 • BORNO

Uku daga cikin ‘yan Majalisun tarayya 10 na Jihar ta Bono, ba sa sa ran komowa kujerun su, domin duk sun gaza samun tikitin Jam’iyyun su a zaben fitar da gwani.

Su ne kuwa, Asabe Bilita, Muhammed Sheriff da Ayuba Bello.

 

 • DELTA

Uku daga cikin ‘yan Majalisun tarayya na Jihar ta Delta ba za su koma kujerun su ba, domin sun fadi a zabukan fitar da gwani.

Su ne: Onyemaecho Mrakpor, Idisi Lobette da Daniel Reyanju.

 

 • EBONYI

Dan Majalisa guda daga cikin 6 na ‘yan Majalisun wakilai na Jihar, tabbas ba zai komo Majalisar ba a zama na gaba.

Shi ne kuwa, Linus Okorie, mai wakiltar mazabar, Ibo/Ohaozara/Onicha, ya kasa samun tikitin Jam’iyyar a zaben fitar da gwani.

 

 • EDO

Lamarin ‘yan Majalisun na Jihar Edo yana da bambanci da na sauran.

Mataimakin mai tsawatarwa na Majalisar, Pally Iriase, ba zai komo Majalisar ba a 2019, saboda sam ma bai tsaya a zaben ba, a sabili da yarjejeniyar da suka cimma a mazabar na shi.

 

 • EKITI

Daya daga cikin ‘yan Majalisun Jihar Ekiti, ba zai komo Majalisar ba.

Shi ne kuwa, Olamide Johnson, mai wakiltar, Ijero/Ekiti West/Efon, ya kasa samun amincewar Jam’iyyar na shi a zaben fitar da gwani.

 

 • ENUGU

Tamkar dai Jihar Ekiti, daya daga cikin ‘yan Majalisun tarayya na Jihar ta Enugu, ba zai komo Majalisar ba a 2019.

Shi ne kuwa, Chukwuemeka Ujam, wanda ya shiga Majalisar a karo na farko, shi ma bai sami tikitin Jam’iyyar ne ba a zaben fitar da gwani.

 

 • FCT

Duk ‘yan Majalisun tarayya biyu daga babban birnin tarayyan ba za su komo kan kujerun na su ba.

Su ne kuwa, Zephaniah Jisalo da, Zakari Angulu, duk sun nemi tikitin yin takara ne a majalisar Dattijai. Har yanzun dai babu tabbacin ko wane ne zai gwabza da Philip Aduda na Jam’iyyar PDP a cikin su.

 

 • EBONYI

Daya daga cikin ‘yan Majalisun tarayya 6 na Jihar ta Ebonyi, ba zai komo Majalisar ba.

Shi ne ko, Linus Okorie, mai wakiltar mazabar Ibo/Ohaozara/Onicha, bai sami tikitin Jam’iyyar ba a zaben fitar da gwani.

 

 • GOMBE

Biyu daga cikin ‘yan Majalisun tarayya 6 na Jihar ta Gombe, akwai tabbacin ba za su komo Majalisar ba a 2019.

Mataimakiyar shugaban marasa rinjaye, Binta Bello, ba ta sami tikitin Jam’iyyar ta PDP ba, a zaben fitar da gwani, sa’ilin da shi ma Samaila Kashena, ya fadi a zaben na fitar da gwani.

 

 • IMO

Biyu daga cikin ‘yan Majalisun tarayya daga Jihar ta Imo, 10, ba za su koma Majalisar ba a karo na gaba, duk a dalilan hakan.

Biyun su ne, Chukwukere Austin da Goodluck Opiah, duk sun fadi a zaben fitar da gwani.

 

 • JIGAWA

A Jihar Jigawa, uku daga cikin 11 na ‘yan Majalisun tarayya ba za su koma Majalisar ba a 2019, domin duk sun fadi a zabukan fitar da gwani.

Su ne,  Sani Zorro, Rabiu Kaugama da Muhammed Boyi.

 

 • KADUNA

A duk Jihohi 36 da babban birnin tarayya, Jihar Kaduna ce ke da mafiya yawan ‘yan Majalisun tarayya da ba za su koma a kan kujerun su ba, a karo na gaba.

‘Yan Majalisun bakwai su ne,  Adams Jagaba, Muhammad Soba, Sunday Marshal, Muhammed Abubakar, Yusuf Bala, Mohammed Usman da Lawal Rabiu.

Mista Jagaba, ya fadi ne a Jam’iyyar PDP, a zaben fitar da gwani, shi kuwa, Mista Marshal, ya tsaya ne a takarar mataimakin Gwamna a Jam’iyyar ta PDP, tare da Isa Ashiru.

Sauran duk sun fadi ne a zabukan fitar da gwani.

 

 • KANO

Hudu daga cikin ‘yan Majalisun tarayya 24 na Jihar ta Kano, ba za su koma Majalisar ta tarayya ba.

Hudun su ne, Aliyu Madaki, na Jam’iyyar PDP a Kano ta tsakiya, wanda a yanzun shi ne dan takarar Jam’iyyar ta PDP na Majalisar Dattawa a Kano ta tsakiya, Bashir Baballe, wanda bai tsaya takaran komai ba, da Nasiru Baballe da Mukhtar Chiromawa, wadanda duk sun rasa samun tikitin Jam’iyyun su ne a zaben fitar da gwani.

 

 • KATSINA

Ya zuwa yanzun, dan Majalisar ta wakilai guda ne ake da tabbacin ba zai koma Majalisar ba.

Shi ne kuwa, Aliyu Sani, wanda ya rasa samun tikitin Jam’iyyar  ta APC a zaben fitar da gwani.

 

 • KOGI

A Jihar Kogi, tabbace yake, dan Majalisar ta tarayya guda ne ba zai koma Majalisar ba a 2019.

Shi ne kuwa, Sunday Karimi, ya yi takaran dan majaisar Dattawa ne a Kogi ta Yamma a Jam’iyyar PDP, ya kuma rasa kujrar ga Dino Melaye.

 

 • KWARA

Daga cikin ‘yan Majalisun tarayya 6 daga Jihar Kwara, akwai tabbacin uku ba za su koma Majalisar ba a karo na gaba.

Su ne kuwa,   Razak Atunwa, wanda zai yi takarar kujerar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP, Zakari Mohammed, wanda zai yi takaran Majalisar Dattawa a Kwara ta Arewa a Jam’iyyar PDP, da Amuda Kanike, wanda bai ma shiga takaran fitar da gwanin ba.

 

 • LAGOS

Shida daga cikin ‘yan Majalisun tarayya 24 na Jihar ta Legas tabbas ba za a yi Majailisar ta gaba da su ba.

Su ne,  Tony Nwulu, Adaranijo Abiodun, Joseph Adebayo, Bamgbose Joseph da Diya Babafemi.

Baya ga,  Tony Nwulu, wanda ya tsaya neman takaran Gwamna a Jihar Imo, a karkashin Jam’iyyar UPP, sauran duk sun gaza samun tikitin Jam’iyyar ne a zabukan fitar da gwani.

 

 • NASARAWA

Daga cikin ‘yan Majalisun tarayya biyar daga Jihar Nasarawa, biyu daga cikin su ne kadai ake sa ran komawar su Majalisar ta wakilai a zama na gaba.

Sauran ukun da ba za su dawo ba su ne, Dabid Ombugadu, Mohammed Onawo da Jaafar Ibrahim.

Mista Ombugadu, zai yi wa Jam’iyyar PDP takaran Gwamna ne, a bisa rakiyar Mista Onawo, a babban zaben mai zuwa. Na ukun kuwa, Jaafar Ibrahim, ya kasa samun tikitin Jam’iyyar APC ne a zaben fitar da gwani na takaran Gwamna.

 

 • NEJA

Duk da rudamin da ke a Jihar ta Neja, akwai tabbacin ‘yan Majalisu uku daga Jihar ba za su koma Majalisar ta Tarayya ba a 2019.

Su ne kuwa, Adamu Chika, Faruk Muhammadu da Saleh Shehu, duk sun fadi ne a zaben fitar da gwani.

 

 • OGUN

Biyu ne daga cikin ‘yan Majalisun wakilai na Jihar Ogun, suka fadi a zaben fitar da gwani

Su ne, Olusegun Williams da Kehinde Olusegun.

 

 • ONDO

Daga cikin ‘yan Majalisun Jihar ta Ondo, 9 uku daga cikin su akwai tabbacin ba za su koma Majalisar ba a karo na gaba, saboda faduwar da suka yi a zaben fitar da gwani.

Su ne kuwa, Babatunde Kolawole, Baderinwa Samson da Akinfolarin Mayowa.

 

 • OSUN

A Jihar Osun, Mataimakin Kakakin Majalisar, Yusuf  Lasun, ba zai koma Majalisar ba, a karo na gaba.

Sam bai yi takara ba.

Ya dai tsaya a zaben fitar da gwani na Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC, kuma bai yi nasara ba, Gboyega Isyaka, ne ya kayar da shi.

 

 • OYO

Biyu daga cikin ‘yan Majalisun tarayya na Jihar ba za su koma Majalisar ba a 2019, saboda sun fadi a zabukan fitar da gwani.

Su ne, Ayoade Ojoawo da Oladele George.

 

 • FILATO

A Jihar Filato, biyu daga cikin ‘yan Majalisar Wakilai na tarayya sun tsaya ne a takaran neman shiga Majalisar Dattawa, daya daga cikin su ya fadi a zaben fitar da gwani, dayan kuwa ya fadi ne a neman komawa kujerar na shi a zaben na fitar da gwani.

Edward Pwajok, shugaban kwamitin Majalisar a kan bin doka da harkokin Majalisar, ya tsaya takaran Majalisar Dattawa ne, kuma ya fadi, shi kuwa, Istifanus Gyang, zai tsaya wa Jam’iyyar PDP takara ne a mazabar Majalisar Dattawa ta Filato ta Arewa.

Suleiman Yahaya-Kwande, ya fadi ne a kokarin sa na komawa Majalisar a karo na uku.

 

 • RIBAS

Biyu daga cikin ‘yan majalisun na tarayya daga Jihar Ribas, ana da tabbacin rashin komawar su ciki Majalisar a karo na gaba.

Su ne kuwa, Chidi Frank, ya fadi a zaben fitar da gwani, da, Betty Apiafi, wacce ta tsaya takaran kujerar Majalisar Dattawa.

 

 • TARABA

Wakili guda ne aka tabbatar ba zai koma Majalisar ba a karo na gaba daga Jihar ta Taraba, sabili da faduwan da ya yi a zaben fitar da gwani.

Shi ne kuwa, Malle Ibrahim, mai wakiltar mazabar, Jalingo/Yorro/Zing, a Majalisar wakilan ta tarayya.

 

 • YOBE

A Jihar Yobe, dan majaisar tarayya mai wakiltar mazabar Fika/Fune, a majalisar ta tarayya, Ismail Gadaka, ba zai koma Majalisar ba, domin ya fadi a zaben fitar da gwani.

 

 • ZAMFARA

A bisa rudamin da ya kacame a Jihar ta Zamfara, duk ‘yan Majalisun Jihar da ke karkashin Jam’iyyar APC, ba za su koma Majalisar ba a zaman majalisar na gaba. Kasantuwar kin amincewar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi na karban duk sunayen da aka gabatar mata daga Jihar ta Zamfara, daga Jam’iyyar ta APC.

Hukumar zaben ta ce Jam’iyyar ta APC ba ta da hurumin gabatar da kowa daga Jihar ta Zamfara saboda ta kasa gudanar da zabukan fitar da gwani a lokutan da aka kayyade mata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!