Connect with us

LABARAI

Mahara Sun Shafe Yini Cur Suna Luguden Wuta A Zamfara

Published

on

Al’ummar garin Kaka, da ke Karamar Hukumar Birnin magaji, ta Jihar Zamfara, na cikin tsaka mai wuya, sakamakon yanda mahara suka kwashe awa Ashirin da hudu suna cin Karensu babu babbaka.

Garin na Kaka, tsakanin sa da shalkwatar karamar Hukumar Birnin Magaji, bai wuce Kilomita Takwas ba, a rahotan da muke samu daga makwabtan garin, da suka yiwo hijira zuwa cikin garin Birnin Magajin, sun bayyana cewa “aman bindigogi ne kawai kake ji babu kakkautawa.

Haka-kazalika ma a Garin Daban, da ke karkashin Masarautar Kwatar Kwashi cikin Karamar Hukumar Bungudu, a jiya mahara sun kashe mutane biyu kuma sun yi awan gaba da dabobin su gaba daya.

A ranar Laraba kuma, maharan sun kai farmaki a wasu kauyakun na karamar hukumar ta Birnin Magaji, ta Jihar  Zamfara, inda suka kashe mazauna kauyakun masu yawa. Wasu daga cikin wadanda suka kashen sun taras da su ne suna aiki a cikin gonakin su inda suka far masu da kisa.

Wata majiyar ta ce, ‘yan ta’addan sun zo ne dauke da muggan makamai da rana tsaka misalin karfe daya na rana suka kuma bude wuta a kan wasu manoman da suke hakan dankalin Turawa a garin, Garin Haladu.

Wani mazaunin garin ya ce, “Sun kashe mutane 10 a Garin Haladu, a wannan farmakin da suka kai.

Ya kara da cewa, “sun sake dawowa da yammaci, suka tayar da wasu kauyaku da ke sassan.”

Majiyar ta ce, a harin da suka kawo a ranar ta Laraba, sun kashe mutane 12 ne a Garin Haladu. Hakanan a kauyan Nasarawa Godal, sun kashe mutane hudu, sa’ilin da suka kashe mutane tara a kauyan Garin Kaka, in ji shi. Duk kauyakun uku suna karamar hukuma guda ne.

“Da yawan matasa a garin na Nasarawa Godal, duk sun gudu ne zuwa Garin Haladu, domin su taimaka wa makwabtan na su yakan ‘yan ta’addan. Daga cikin su, ‘yan ta’addan sun kashe mutane hudu, wadanda sai a ranar Alhamis ne aka iya gano gawarwakin su,” in ji majiyar.

Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta domin dalilai na tsaro, ta ambaci wadanda aka kashen sun fito ne daga garin Nasarawa Godal, su ne, Kurma Garba, Sunusi Mairoba, Ibrahim Yahuza da Haruna Dangodal.

Tuni an yi jana’izan wadannan hudun.

Da yawa kuma sun jikkata, suna kuma amsan magani a Asibitin Nasarawa Godal, in ji majiyar.

Wadanda kuma na su raunukan suka kazanta an wuce da su babban Asibitin Kauran Namoda.

Karamar hukumar ta Birnin Magaji, nan ne Ministan tsaro, Mansur [an Ali ya fito.

Yawancin garuruwan da ke kewayen Birnin Magajin kamar su, Ballaka, Tsalle, Gidan Kare, Katsinawa, Garin Boka da Garin kaka, duk al’umma sun kaurace masu a sakamakon hare-haren na ‘yan ta’addan. Mazauna kauyakun duk suna gudun hijira ne a yanzun haka a shakkwatar karamar hukumar.

Majiyar ta ce a yanzun haka, mazauna yankunan suna ta bin dazuka ne domin kwaso gawarwaki, wanda hakan ke nuna akwai yiwuwar yawan wadanda aka kashen su zarta abin da ake fada.

Sojoji sun isa yankin ne awanni bayan tafiyan maharan a motoci uku.

Da yawan kananan hukumomi a Jihar ta Zamfara suna ta fama da hare-haren ‘yan ta’addan da kuma barayin shanu, inda kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Shankafi, Maradun, Maru da Birnin Magaji, a matsayin wuraren da lamarin yafi shafa.

Ko da wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ta Zamfara, Muhammad Shehu, bai amsa wayar wakilin namu ba, bai kuma maido da amsar sakonnin da ya aike masa ba.

[aruruwan mutane ne ‘yan ta’addan suka kashe a hare-haren da suke kaiwa Jihar ta Zamfara a wannan shekarar ta 2018. Hare-haren kuma sun ci gaba, duk da jibgin Jami’an tsaron da aka jibge a Jihar.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!