Connect with us

BIDIYO

Dalilin Da Ya Sa Na Kafa Gidauniyar Tallafa Wa Mabuqata – Rashida Maisa’a

Published

on

Dalilin Da Ya Sa Na Kafa Gidauniyar Tallafa Wa Mabuqata – Rashida Maisa’a

Daga Wakilinmu, Kano

 

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, RASHIDA ADAMU MAISA’A, wadda aka fi sani da Rashida mai sa’a, ta yi fice a wajen tallafawa marayu da sauran mabuqata a gidaunaiyarta Mai Sa’a Charity kuma a qarqashin wannan Gidauniyar tata mabuqata masu yawa sun samu ‘yanci ta hanyar ba su ilimi da samar musu da lafiya da sauran abubuwan buqata inda take shiga lungu da saqo don ganin ta warware matsalolin mabuqata.

A zantawarsu da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI a Kano, Rashida Mai Sa’a ta yi bayani a kan tsawon lokacin da ta yi tana gudanar da Gidauniyar tata, da kuma yadda ta fara gudanar da harkokin nata har ma da nasarorin da ta samu. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasanace.

 

To, Rashida za mu so ki sanar da masu karatu yadda a ka yi ki ka samar da Gidauniyarki ta Maisa’a Charity da kuma abubuwan da ki ke gudanarwa a gidauniyar?

To, ita dai wannan gdauniya tawa ina ganin na kafa ta ne yau kusan shekaru takwas kenan. Kodayake a baya da na kafa ban yi  mata suna ba, ina yin abubuwa ne haka na tamako sai na ga akwai buqatar na rinqa tafiya da zamani, don haka sai na mayar da shi a matsayin Gidauniya, na yi mata suna na ci gaba da yin abubuwa da sunan Gidauniyar ina taimaka wa marasa qarfi, idan mutum ba shi da lafiya  na kai shi asibiti kuma nakan shiga asibiti duka na ji xakin yara masu yoyin fitsari ina kai musu tallafi kuma sai ya zama na buxe abin na xauki ma’aikata da za mu rinqa yin aiki da su, sai kuma na gano akwai mutanen da suke son tallafa wa jama’a. Sai dai ba su da qafar da za su bayar, wasu kuma suna son su yi tallafin amma ba su da kuxin da za su yi, to a haka sai muka haxu wasu su bayar kuma wasu da ba su da hali bayarwa sai su zo mu tafi mu raba kayan tallafin da su. Ka ga sun yi da qarfinsu. Muna shiga lungu da qauyuka kamar wajen ‘yan gudun hijira muna kai musu kayan abinci da kayan sakawa da magunguna, har muna yin gwaji na cutar HIV da qwayar polio mu haxa kai da qungiyar lafiya, kuma muna qoqarin gyara kamar  saka rufin kwano da tabarmi da butoci har ma da fanka kuma muna samar da makarantun Islamiyya don akwai wani qauye da muka kai tallafi na sabulu da omo to akwai wata mata da ta tashi ta xaga hannu ta ce ita ba burin da take da hsi ta kai  shekara 40, amma ba ta iya fatiha ba, don haka suna son mu kawo musu malaman addini da za su rinqa koyar da su. To a wannan waje a take muka nemi mai unguwa  ya sahhale mana mu yi makaranta ta Islamiyya ta langa-langa, kafin mu samu damar da za mu gina musu. Haka kuma aka yi aka samar musu na zo cikin gari na samar musu da malamar da ake zuwa tana koyar da su. To yanzu an kusa shekara guda kenan ana ba su ilimi a yanzu har mun zama ‘yan’uwa da su. Har kayan miya za ka ga sun aiko min kwandon tumatur.

 

To, a yanzu ya ya tafiyar da gidauniyar take idan kika kwatanta da ta baya?

E, a yanzu an samu ci gaba sosai ka ga da ni kaxai ce don abin d ana samu shi ne nake yin hidima da shi, amma yanzu da na samu muqamin gwamnati a matsayina na mai ba Gwamna shawara a kan harkar mata ka ga samun kuxina ya qaru, kuma ina  bin manyan mutane waxanda ba za su iya fitowa da kansu su yi ba in bi ina kai wa mutane takard na neman taimako don akwai buqaar da z ata taso wadda ta fi qarfinmu. Sai mu rubuta takarda mu kai wa masu hali, kuma ckin hikimar Allah duk inda muka je ba ma rasawa.

 

A wannan aikin da kike yi kowanne mara lafiya ne kika samu wanda kika matsu ko ta halin qaqa ki ga an samu taimako don ya samu lafya?

To akwai wani yaro wanda na san maganarsa ta yaxu a Kano har sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya je ya duba yaron za a yi masa aikin qoda. Watarana mun dawo daga wani qauye wjaen rabon tallafi sai na ce mu bi ta sibitin Nassarawa don mu duba jikin yaron. Muka je muka tambaya mene ne matsalar sa? Aka ce za a yi masa dashen qoda naira miliyan goma sha xaya. Cikin ikon Allah da na zo na saka abin a cikin shafina ina jin sha biyu na dare na saka, amma qarfe uku na dare sai ga wani mutum daga qasar Jamus ya ce na tura masa komai na asibitun da kuma aikin da za a yi masa, da kuma kuxin da za a kashe a aikin, amma wani al’amari na Allah bayan mun je mun gama magana iyayensa sun ba da asusun ajiyarsu Allah ya yi wa yaron rasuwa, kuma mun qara samun wani mutum ana da ciwon qoda yana da ciwon suga da HIV kuma yana da kansa ta cikin jini, to ana son a fita da shi zuwa Indiya, don yi masa magani, sia na sanar da wannan mutumin ga halin da wannan ake ciki kwanaki uku ya turo da miliyan bakwai sai aka shirya tafiya wannan mara lafiya sai da ya kai wata uku a indiya Allah ya sa ya rabu da ciwon duka, a yanzu mutumin yana cikin  qoshin lafiya, kuma kullum yana yi min fatan alheri. A yanzu ma da shi muke harkar raba kayan tallafi na gidauniyata. Don daga wannan ya kawo min wasu marasa lafiya an nema musu magani.

 

Ko wane irin nasarori ki ka samu a rayuwarki ta vangaren tallafawa jama’a da ki ke yi?

To babbar nasara ita ce sa farin cikin zuciyoyi don a  duk lokacin da tallafa wa jama’a na kan samu kaina cikin farin ciki, kuma na samu lambobin yabo da dama da aka karrama ni da su har ma London na je na karvi lambar girmamawa, kuma nan gaba kaxan zan je qasar Jamus shi ya sa kullum muke  buxa abin don yanzu akwai kaya da muka xinka na ‘yanmata da yara wanda za mu kai Tudun Maliki gidan masu tavin hankali. Akwai ‘yanmata da smaari da uske buqata haka akwai wata uwar marayu da ita ma za mu kai mata baiwa yara don su yi hidimar maulidi don tunawa da haihuwar fiyayyen halitta.

 

Wasu qungitoin idan suna neman tallafi na mara lafiya akan turo musu kuxin ta asusun ajiyarsu ke ma haka ne?

To haskiya ni ba haka ba ne, nakan tura asusun ajiyar ‘yan’uwa ko iyayen ma buqata ne, idan na tura nawa ka ga yau ba ka san yadda rayuwa za ta kasnace ba to idan ta Allah ta kasance sai abin ya zama da matsala, don haka ba na yin amfani da asusun ajiyata kuma duk kuxin da muke samu ba ma amfani da shi a buqatar kanmu sai dai mu tura ga masu buqata.

 

Daga qarshe mene ne fatanki na qarshe a game da wannan gidauniya taki?

Fatana shi ne har ‘ya’yana da jikokina su gaji abin da nake yi kuma ina godiya ga xumbin jama’a da suke ba da gudunmuwa musamman Gwamnatin Kano da sauran jama’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: