Connect with us

MANYAN LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Jagoran APC Da Mutum 19 A Zamfara

Published

on

‘Yan ta’adda sun dawo da hare hare a jihar Zamfara, inda saka kashe mutum 20 ciki har da jagoran jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Aliyu Abbas.
‘Yan ta’adda sun kai hai garin Magami dake karamar hukumar Maradun inda suka budewa magayyin wuta ya kuma mutu na take, wani da aka yi abin a gabansa ya bayyana cewa, bayan da suka kashe Abbas ne suka kuma bude wuka a kan jama’a in da mutm 20 suka riga mu gidan gaskiya.
Sarkin Maradun, Alhaji Garba Tambari ya yi wa mukaddashin gwamnan da sauran manyan jami’a rundunonin tsaron jihar cewa, jami’an tsaron dake yakan ‘yan ta’addan suna dari dari da ayyukansu, ba sa aikin da yadda ya kamata.
Ya yi mamakin yadda jami’an tsaron ke gudun yin gaba da gaba da ‘yan ta’addan a duk lokacin da suka kawo hari.
“Muna kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’adda ga jami’an tsaron amma babu wani mataki da aka dauka na kawo karshen ta’addancin da suke yi “, inji shi.

Ya kuma kara da cewa, lokaci ya yi da jami’an tsaro za su yi azamar ganin kawo karshen ‘yan ta’addan a jihar zamfara gaba daya.
Sarkin ya kuma bayyana cewa, a haka yanzu garuruwa da kauyuka da daman a karkashin mulkin ‘yan ta’adda.
Shugaban karamar hukumar, Hon. Yahya Shehu ya nuna damuwarsa a kan ayyukan da jamoi’an tsaron ke yi a jihar.
Ya kuma bayyana cewa, jama’a sun kauracewa garuruwa da kauyuka fiye da 20 a jihar saboda harkokin ‘yan ta’adda.
Shi kuma mukadashin gwamnan jihar, Hon. Sanusi Garba Rikiji ya yi tir ne da ayyukan ‘yan ta’adan, ya kuma bukaci a dauki mataki na musamman doin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.
Ya ce, duk da kawo rundunar sojoji na ‘One Battalion Brigade’ daga Sakkwato zuwa Gusau harkokin ‘yan ta’adda ya ci gaba da bunkasa ba tare da kakkauta wa ba.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar na iya ka kokarinta na samar wa da jami’an tsaron dukkan kayayakin da suke bukata don gudanar da ayyukansu, ya kuma yi alkawarin haduwa da dukkan masu ruwa da tsaki don sake tsarin yadda za a fitowa lamarin ‘yan ta’addan a gaggawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!