Connect with us

MAKALAR YAU

Zaben 2019: Sabon Salon Siyasar Tara Mutane A Nijeriya

Published

on

Akullun yaumul ana kara ganin sabon abu a siyasar Nijeriya, wani lokacin abin ya burgeka wani lokaci kuma ya bata maka rai, kai wani lokaci ma ka rasa wane zaka dauka bacin rai ko kuwa burgewa.
A shekarar 2015 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zo da wani sabon salon siyasar tara mutane wanda haka ba karamin tasiri ya yi ba a nasarar da ya samu, wannan taron jama’a ya tada hankalin masu mulki a wancan lokacin sannan ya kara masa kwarin gwuiwar samun nasara.
Sannu a hankali wannan sai gashi wannan ya zama wani bangare na koyi da siysarsa musamman lokacin da ya ci zabe, a duk lokacin zai bar babban birnin tarayya Abuja ya je wata jaha, abin da zaka fara lura da shi a wannan wuri shi ne irin jama’ar da suka taru ko kuma aka tare domin yi masa lalai marhabin.
Sannan tara jama’ar kan shi ya kasu kashi biyu akwai wadanda suke taruwa saboda tsananin soyayyarsu ga shugaba Muhammadu Buhari akwai kuma wadanda ake tara masa idan zai kai ziyara wata jana duba da cewa yanzu yana son ya ga taron jama’a idan zai zo wuri
Ko shakka bubu shugaban kasa Muhammadu Buhari yana son idan ya zo waje ya ga mutane sun taro sun yi dafifi iyakar ganin mutum, wannan yasa masu siyasar burgewa ko ba su da jama’a suna yin kokarin wajen ganin sun yo hayar mutane da za su fitar da su kunya in dai aka ce shugaban kasa zai zo waje.
Tun ba a yi nisa ba, hakan ya zama wata babbar al’adar ‘yan siyasa a matakin jaha da kananan hukumomi, suna da sha’awar su ga sun tara mutane ko da kuwa wadannan mutane ba su da katin zabe.
Wannan ya tuna mani lokacin da gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari yake yakin neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi a matsayin dan takarar ta a zaben 2015, duk lokacin da aka kawo masa mutane domin su nuna goyan bayansu gare shi, babar tambayar da yake yi masu a wannan lokaci ita ce daligat ne ko?
Duk wanda ya amsa da a’a to baya cikin irin jerin mutane da yake bukata a wannan lokaci kuma nan take zai sanar da kai cewa lokacin amfaninka bai kai ga zuwa ba amma da zaran ya samu nasarar cinye zaben fidda gwani to za a nemoka.
Haka ta ci gaba da faruwa a duk lokacin da ‘yan kwanta-kwanta za su kwaso jama’a zuwa wajensa a wancan lokacin in dai kai ba daligat bane nan take zai sanar da kai cewa ba yanzu bane lokacin amfaninka ba, duk wanda yake zuwa wajen gwamna Masari hira kafin ya zama gwamna ya san haka.
Abin da yasa na bada misali da gwamna Masari shi ne, mafiyawan ‘yan siyasar da ke son taron jama’a ba su lura da cewa mutanen da suke tarawa suna da amfani na kusa ko kuwa sai nan gaba, domin idan za ka tara mutum miliyan daya amma dubu dari kaiwa da ke katin zabe ya za a kira wannan taron ke nan?
Duk kawan ja ce, shi kansu shugaban kasa Muhammadu Buhari yana son jama’ar ne ba tare da yin la’akari da cewa suna da katin zabe ba wanda da shi ne idan suka jefa masa kuri’a zai iya samun nasara a lokacin zabe.
Tunda tara jama’a ya yi babban tasiri a zuciyar ‘yan siyasa kuma suna alfahari da haka, to yana da wahalar gaske a iya canza wannan sabon tsari da wuri, sannan ba zaka iya yi wa dan siyasa hannunka mai sanda da wani batu sabanin ka tara masa jama’a ko da kuwa basu da katin jefa kuri’a a ranar zabe.
Idan kuwa haka ne, wannan ya nuna cewa da yawan ‘yan siyasa masu wayewar a tara jama’a a filin taro suna bisa igiyar ruwa, wanda sai lokacin zabe ko kuma ma ranar zabe su kasa fita daga cikin kogin da ya taho da su, inda a karshe dai sai ka ji ana yi wa mutum jaje da wasu shawarwari da ba su da amfani a wannan lokaci.
Haka kuma idan muka koma a bangaran shugaban kasa wanda muna iya cewa tara jama’a a lokacin wani taro ko yakin neman zabe al’adarsa ce, wannan kuwa ko mutum na so ko baya so, Buhari yana da jama’ar da suke kaunarsa ta Allah da Annabi akwai kuma wadanda ke zuwa wajen da zai yi taro domin kawai su ganshi ko su ga taro, akwai kuma wadanda ke zuwa domin sanin abin da za su nan gaba.
Na yi imanin cewa daga yanzu duk jahar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je in dai ba a tara jama’a ba, to daga nan zai tabbatarwa da kansa cewa ya fadi a wannan jahar, sai dai kuma a zahiri ba haka bane, amma saboda tasirin abin da na ambata a baya sai anyi hakan za a faranta masa.
Suma a bangaran ‘yan adawa su gano cewa tara jama’a a lokacin taro yana da matukar tasiri a siyasar Nijeriya saboda haka suka fara aron hannu domin nuna kwarin kashinsu da masu rike da madafun iko, tunda bida ta ga rana suma yanzu za su tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.
Wannan tasa duk lokacin da wata jam’iyyar adawa ta yi wani taro ya kwashi jama’a sai ka ji ana alakanta ta da irin taro su shugaba Muhammadu Buhari, ko kuma wanda bai sani ba ya ce shi ne da kanshi Buharin.
Taron da dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku abubkar ya yi a jihar Sakwato a matsayin taron farko na bude yakin neman zabensa ya tayar da muhawara musamman jama’ar da suka taro a wannan wuri.
Kamar yadda na ce akwai kashi kashi na jama’ar da ke taruwa a wajen taro a kwai wadanda ke zuwa domin ganin yadda za akare akwai wadanda suke zuwa domin nuna soyayya akwai kuma wadanda ake biya domin su je su cika filin taro wanda shi ke ba jama’a tsoro da su kan su ‘yan siyasar
Tun anar da aka yi wannan taro aka fara tafka muhawara akan jama’ar da suka taro a garin Sakwato dalili kuwa shi ne, lokacin tsohon gwamnan jihar Sakwato Alu Magatarkardar Wamakko ya shiga garin Sakwato domin nuna biyayyarsa ga shugaba Buhari da jam’iyyar APC an ga yadda jama’a suka fitar farin dan go a matsayinsa na dan adawa a wannan jiha.
Anan cikin haka sai wannan taro na jam’iyyar adawa a tarayyar Nijeriya da ta shirya kamar daga sama sai kawai muka ji gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i ya fito fili yana cewa lallai wannan taron an dauko hayar bakin haure ne daga jamhuriyar Nijar ma’ana dai wadanda suka yi wannan taro ana nuna kamar ba su isa ba.
Ba tare da bata lokaci ba sai ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi taron karbar wasu jiga jigar jam’iyyar PDP zuwa APC inda ya bayyana cewa sun tara mutane fiya da miliyan biyar a filin wasa kwallon kafa na Sani Abacha da ke Kano.
Wannan ma ya tayar da babbar muhawara inda wasu ke ganin shi kanshi filin wasan mutum dubu 16 kawai yake dauka amma gashi an tara mutum miliyan biyar to ya abin yake?
Sakamakon wannan al’amari masana harkokin siyasa na ganin da wannan tara jama’ar ne za a yi wa mafi yawan ‘yan siyasa fafalolo a lokacin yakin neman zabe ciki kuwa harda shugaban kasa Buhari domin ta fara bayyana a kwanan nan lokacin da yakai wata ziyara a jihar Barno a maimakon jama’ar da ake gani sun yi dafifi a bakin hanya suna yi masa lalai marhabin sai dai kawai aka ga ‘yan makaranta suna daga masa hannu.
Hakan yana kara tabbatar da cewa lallai dole ‘yan siyasa su fara karatun ta nustu game da batun tara jama’a in kuma ba haka ba, za ayi masu sakiyar da ba ruwa a tara masu jama’a amma wadanda ba su da kuri’ar da za su jefa a ranar zabe.
To amma ko ma dai menene, Baba Buhari ne amsa, domin shi ke da wannan sabon salon siyasa, kuma yana ji da shi, sannan da shi ake sa ran yi masa aika-aika idan bai farga ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!