Connect with us

RA'AYINMU

Gurbata Yanayi Babbar Illa Ce Ga Rayuwar Al’umma

Published

on

Rahotanni daga Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) sun nuna cewa, a kalla gurbata muhalli na sanadiyyar salwantar rayukan kusan mutum miliyan goma a duniya a kowace shekara.

Wani babban abin tashin hankalin shi ne Nijeriya na daga cikin kasashen Afirkan da wannan matsala ta yi kamari a cikinta, kuma ita ce ta hudu a cikin jerin kasashen duniya da ake fama da wannan matsala ta gurbata muhalli. Domin kuwa kididdiga ta nuna cewa, duk cikin ‘yan Nijeriya dubu dari, akwai mutum dari da hamsin da ke mutuwa sakamakon shakar gurbatacciyar iska a kwace shekara.

A kasar Afganistan mutum 406, a Pakistan 207, a Indiya 195 ke mutuwa daga cikin mutum 100,000 a kowace shekara, in aka kwatanta da Nijeriya sai a ga abin ba kyau. Hattana kasashen da suke da manyan masana’antu za ka ga akwai dama-dama, kasashe irin su Chana wadda mutum 117 ke mutuwa daga cikin mutum 100,000; Rasha mutum 62; Jamane mutum 22; Tarayyar Turai 21; Amurka, 21; Jafan, 13, sai kuma Kanada mai mutum 12.

Kamar yadda wani rahoton shekara da ya fito daga  “Health Effectibe Institute” wanda mujallar “Global Air Report” ta wallafa ya nuna cewa, Nijeriya da wasu kasashe 10 na daga cikin muhallin da za a iya shakar gurba tacciyar iskar da za a mutu, sakamakon amfani janaratoci da hayakin da ababen hawa ke fitarwa da kona daji da kona shara da makamantansu. Sannan kuma daga cikin abubuwan da ke gurbata iskar akwai yoyon iskar Gas kamar abin da ke faruwa a jihar Ribas da wasu makwabtanta.

A rahoton WHO na shekara ta 2016 ya nuna cewa, Anaca da Kaduna da Aba da Umuahiya na daga cikin manyan birane 20 a Afirka da suka fi fama da gurbacewar iska.

Haka kuma rahoton ya ci gaba da cewa, kusan birane 3,000 da ke fadin duniya, akalla wadanda ke da yawan jama’ar da suka kai mutum miliyan 100,000 ke fama da matsalar gurbacewar iska. Bugu da kari kuma an bayyana cewa, garin birnin Kaduna da Aba da Umaahiya da ke da matsayin na 8 da 9 da kuma 19 daga cikin birane 20 na fama da gurbacewar iska.

Masana sun nuna cewa akwai nau’I iri biyu na gurbacewar iska- gurbacewa ta hanyar iskar Gas da kuma hayaki. Kowane nau’I daga cikinsu babbar illa ne, musamman ga rayuwar kananan yara. Bincike ya nuna cewa kashi 93 daga cikin kasha 100 na yara ‘yan kasa da shekara 15 na shakar gurbatacciyar iska. Haka kuma yaro daya na mutuwa daga cikin yara 4 sakamakon shakar gurbatacciyar iska. Gurbatacciyar iskar ta fi yi wa yaran illa ne saboda suna daurin shakar iska a-kai-a-kai. Bayan kisan yara kanana da gurbatacciyar iskar ke yi tana kuma haifar musu da cututtuka iri daban-daban.

Ga manya kuma, shakar gurbatacciyar iska ita ke haifar da mututar kashi 1 daga cikin kashi 4 na jama’a sakamakon ciwon zuciya, kashi 25 daga cikin 100 sakamakon shanyewar jiki, kashi 43 daga cikin 100 miyagun cututtuka sannan sai kashi 25 daga cutar kansa.

Ida ana shan taba kuma babu abinci mai kyau suka kuma hadu da hawan jini, abu na hudu da zai taimaka wajen kashe mutum it ace gurbatacciyar isaka.

An lura cewa wannan annoba ta gurbacewar iska ta fi yawaita a kasashe masu karanci da matsakaicin tattalin arziki, kamar kasar Asiya da nahiyar Afirka  da kuma kasashen da ke yankin Gabashin tekun Meditireniyan irin su; kasar Turai da Amurka.

Ganin hatsarin da ke tattare da shakar gurbatacciyar iskar tuni kasashen da suka ci gaba suka mike tsaye wajen kawo karshenta kuma sun samu nasara a kan yin hakan, saboda haka yanzu ba sa fuskantar irin wannan barazana ta shakar gurbatacciyar iska.

Shawarwarin da muke bayarwa da kuma fatanmu a nan shi ne masu ruwa da tsaki da ked a alhakin kula dakile hanyoyin gurbacewar iska su fahimci irin mummunar illar da take da ita a cikin al’umma, Sannan kuma su sani cewa, ya zama wajibi su tashi tsaye wajen kawo karshen gurbacewar iska a kasar nan. Haka kuma muna kira da babbar murya ga gwamnati ta samar da hanyoyin da za a kawar da gurbata iska, sannan a hukunta duk wanda ya yi kunnen kasahi ya karya dokar don ya zama darasi ga na baya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!