Connect with us

ADABI

Matsayin Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa Jiya Da Yau: Kalubale Ga Matasan Zamani(5)

Published

on

Gabatarwa:

Mun dauko wa masu karatunmu wannan kasida ta Bashir Aliyu Sallau mai take, ‘Matsayin  Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa Jiya Da Yau: Kalubale Ga Matasan zamani’ daga cikin littafin Champion Of Hausa cikin Hausa, wanda Sashin Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka, na jami’ar Ahmadu Bello ya wallafa domin amfanin masu nazari da kuma sha’awar karatun Hausa da bunkasar al’adun Hausawa.

Matashiya: Wani masani kuma ya bayyana cewa Huasawa su ne mutanen da harshensu dai shi ne Hausa sannan dukkan al’adunsu da ta’adunsu na Hausa ne. Haka kuma addinin Musulinci ya yi cikakken tasiri a kansu (Magaji, 1986:3).

 

Ci gaba daga makon jiya.

Wani tsari mai ban sha’awa dangane da aiwatar da sana’ar wanzanci shi ne wanzami ba shi da iyakar kasar da zai rika gudanar da  ayyukansa. Yana iya fita daga garinsu ko kasar dagacinsu ko hakiminsu kjo sarkinsu, kai a wannan zamanin har jihar su ya tafi wuraren da mutanensa suke domin yi musu ayyukan wanzanci misali, idan Bahaushe ya auri Bafulatana wadda ita al’adarsu mace ba ta yin haihuwar fari a gidan mijinta, sai dai ta tafi goyon ciki gidan mafinta. To, idan ta haihu ba mahaifanta ne za su kira wanzamin ba, mijinta ko mahaifinsa ne zai kira wanzaminsu na gida domin ya yi ayyukan. Haka kuma a wannan zamani idan mutum na aikin gwamnati a wani gari, idan matarsa ta haihu sai ya aiko garinsu don wanzaminsu na gida ya je domin yin ayyukan. Misali, lokacin da nake gudanar da wannan bincike, da na ziyarci Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya na sadu da Dakta Kabir Tsafe, wanda a lokacinsa ne shugaban Sashin koyar da  Tarihi kuma shugaban Tsangayar Fasaha da zamantakewa na wannan jamai’a, a lokacin da nake tattaunawa da shi ya bayyana min cewa, a duk lokacin da aka haiuhu gidansa nan Zariya yana aikawa garinsu Tsafe don yin wanzancinsu na gida ya zo ya yi ayyukan wanzanci. Ni ma a halin yanzu mutanen da nake yi wa aikin wanzamci wadanda kuma muka gaji juna wadanda suke aikin gwamnati a Katsina da Abuja da Kaduna da sauran wurarare, idan matansu suka haihu suna aiko wa in je wadannan garuruwa da suke don yin aikace-aikacen wanzanci.

A wani lokaci takan kama a sauya wanzamin da aka gada. Dalilian da kansa a yi wannan sauyin sun hada da sauyin wurin zama wato idan mai gida ya tashi daga garinsu ya goma wani gari da yake nesa da garinsu na Sali. To a sabon wurin day a sauka idan aka yi masa haihuwa ko yana bukatar a yi wa wasu yaransa kaciya ko dai wata bukata ta aikin wanzanci a gidansa. Sai ya nemi wani wanzami domin ya yi masa wadannan ayyuka. Daga wannan lokaci shi wannan wanzami ya zama na gidansa, sai kuwa idan wani dallin ya tilasta a sauya shi.

Haka kuma idan wanzamin gida ya rasu ko wata larura ta rashin lafiya ta same shi, idan ba shi da mai gadonsa sai wadanda yake yi wa aiki su samu wani wanda zai maye gurbinsa.shi ma daga nanan ya zama wanzamin wannan gida. Idan kuma rashin fahimtar juna ko wani sabani ya shiga tsakanin wanzamin gida da mai gidan da yake yi wa aiki, misali, maita ko siyasa ko aure da sauransu syukan tilasta a sauya wanzami.

Idan ba ta wadannan hanyoyi da aka yi bayaninsu ba, matukar wani wanzami ya yi shisshigi ya shiga gidan da wani wanzami yake yin aiki ba tare da izininsa ba, barna na iya shiga. Domin kuwa kowannensu zai ta kokarin surkulle da sihirce-sihircen domin nakasa abokin hamayyarsa ko ya lalata ayyukan da ya yi.

Wanzaman Hausawa sun kasu gida biyu. Akwai wanzaman gado da wanzaman koko. Wanzaman gado su ne wadanda suka gaji yin sana’ar wanzanci a wajen iyayensu da kakaninsu, kuma suna yin dukkan ayyukan wanzanci wadanda suka hada da yin aski da kaciya da cire belin wuya da cire angurya da bayar da magungunan gargajiya da yin tsagar gado da ta magani da ta kwalliya. Ire-iren wadannan wanzamai ne suke gadon gidajen da za su rika yin ayyukan wanzanci. Haka kuma daga cikin irin su ne ake nada sarkin aska ko magajin aska. Idan bukatar aikinsu ta tashi a ma fi yawancin lokaci gidajensu ake zuwka domin a sanar das u wuri da lokacin da ake so su je don yin ayyukansu. Kuma a mafi yawancin lokaci ire-iren wadannan wanzamai bas u da rainuwa domin kuwa duk abin da aka ba su a matsayin ladan aikinsu, sai s u karba suna yin murna da godiya. An bayyana cewa, dalilin haka shi ne suna yin wadannan ayyukan ne don gado da don ladan da ake biyansu ba.

Su kuma wanzaman koko ba sa yin dukkan ayyukan wanzanci, iyakar ayyukan da suke yi sun hada da aski da gyaran fuska, wanzaman koko barorin wanzaman gado ne. a wani lokaci irinsu na yin kaho, kuma irinsu ne suke yawo da zabira a kasuwanni da cikin garuruwa suna neman wanda za su yi aski ko gyran fuska ko kaho. Haka kuma ire-iren wadannan wanzamai ne suke yin rumfuna a kasuwanni da shaguna a cikin garuruwa domin yi wa mabukata aski da gyaran fuska. Idan suka yi wa mutum ayyukansu suna gaya wa mutum adadain kudin da zai biya ba kamar wanzaman gado ba. Hausawa na yi wa ire-iren wadannan wanzamai kirarai kamar haka:

“Wanzaman kaho, a ci tuwo a yi aski, cire belin wuya da belin mata sai ‘yan gado”.

 

Fawa

Fawa wata sana’a ce wadda ake sayan dabbobi a yanka don samar da nama ga al’umma. Mahauta suna sarrafa nama ta hanyoyi daban-daban wadanda suka hada da balangu da tsire da kilishi da ragadadda da sauransu. Masu yin wannan sana’a suna taimaka wa  al’umma ta hanyoyi da yawa. Sukan sayi dabbobi daga wurin wadanda suke yin kiwo dsa kuma sarrafa naman dabbobin danye ko gasasshe don sayarwa ga masu bukata. wannan dalili ne yasa wannan sana’a take cikin manyan sana’o’in gargajiya na Hausawa. Masu yenta sukan shahara kuna ana yin fataucin naman da aka sarrafa musamman kilishi, zuwa sassan da ke makwabta da kasar Hausa ta kusa ko ta nesa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!