Connect with us

ADABI

Tonon Sililin Mr. Hampher Jakadan Turai A Musulunci

Published

on

Cigaba daga makon shekaranjiya jiya. 

Babi Na Bakwai

Tabbas naji daɗin wannan sirri da Sakataren hukumar mu ya fayyace gareni, sannan bayan na mayar da littafin kuma, sai na shiga sauraron sirri na Uku kamar yadda aka alkawurta.

Daga baya sakataren yake sanar mini cewar wannan sirri yana cikin wasu takaddu ne guda hamsin, masu ɗauke da wasu mukaloli goma sha huɗu da masana suka rubuta akan hanyar ruguza addinin islama.

Ga kaɗan daga abubuwan da mukalolin sukayi magana akai.

 1. Dole ne a samar da haɗin guiwa da yarjejeniya da gwamnatin Rasha domin samun cikakken ikon kutsawa kasashen musulmin dake makwabtaka da ita ta amfani da karfin soji.

Kasashen sun haɗar da Armenia, Tajikistan, Khorasan, da makwabtansu..

An tabbatar da cewar Rasha da Turkiyya nada rawar takawa a hare-haren a matsayinsu na kasashen dake makabtaka dasu.

 1. Dole a samar da haɗin kai da kasar Faransa domin wargaza musulunci a faɗin duniya.
 2. Dole a cusa kiyayya tsakanin gwamnatin Turkiyya da ta Iran. Sannan akwai bukatar a ruruta kishin kasa da kabilanci da akidar ɓangarancin addinai tsakanin al’ummar waɗannan kasashe biyu.
 3. Dole a mallaka ikon wasu yankunan musulmai ga waɗanda ba musulmai ba.

Misali, a baiwa Yahudawa iko da Madina, Kiristoci a basu Aledandaria, Saibawa a basu Imara, Kermanshawa a basu Nusayriya, Hindiyawa a basu Iran, Dzuris a danka musu Tripoli sukuwa Kharijawa abasu Maskat.

Daga nan sai abaiwa kowannensu makaman da zasu rike cikakken iko da wurin tare da faɗaɗa yankuna, tayadda har sai lokaci yazo musulmai basu da koda taku a hannunsu.

 1. Tarwatsa daular Ottoman izuwa jihohi kamar yadda akayiwa India.

Saboda ba za’a iya samun nasarar mulkar su ba har sai an rarraba kawunansu.

Da zarar an rarraba kawunansu kuma tarwatsa su zaiyi sauki.

 1. Dole a gurɓata addinin musulunci ta hanyar cusa shirka a cikinsa da kuma fitar da sabbin addinai daga gareshi.

Misali, a samar da addini ga Mabiya Husain, da Mabiya Mahdi da mabiya Jafar da kuma Mabiya Ali.

Mazaunin addini na ɗaya ya zama Kerbala, na biyu a Isfahan, na uku a Samarra, na huɗunsu a Khorasan.

Daga nan sai a cusa kiyayya da halatta zubda jini a tsakaninsu.

 1. A lasawa musulmai son jindaɗin duniya da bushasha ta yadda zasu tsunduma shangiya, Zinace zinace, caca da sauran manyan laifuka.
 2. A rinka ɗaukar ɗawainiyar kawar da shugabannin musulmai.

Ko kuma mu reni wasu daga cikinsu sannan mu taimakesu su samu shugabanci tayadda zasu rinka aiwatar da muradun hukumar mu ta common wealth.

 1. A hana koyar da larabci a makarantu tunda shine harshen Al-Kur’ani da Hadisai.

A maimakon haka sai a ɗaukaka ƙananun harsuna sama dashi.

 1. A tura bayi zuwa kasashen musulmai su zamo amintattu kuma masu yin hiduma ga shugabannin su, daga nan za’a rinka samun dukkan sirri, za kuma su rinka cika umarnin hukumar mu.
 2. A ƙarawa masu yaɗa adinin kiristanci karfi ta yadda zasu mamaye fannonin likitanci dana injiniyanci.

Sannan a samar da cibiyoyin yaɗa jita-jita da farfaganda da sigar makarantu, asbitoci da wuraren ibadu.

Akwai bukatar samar da wakilai acikin musulunci waɗanda zasu koyi addinin su zamo koluluwa acikinsa, sannan su rinka soke hukunce-hukunce da kuma kone littattafai.

 1. Dole a sanya shakku a zukatan matasan musulmai mazansu da matansu game da gaskiyar addinin. Sannan ayi kokarin shagaltar dasu da saukesu daga turbar addinin ta hanyar wasanni, kallace-kallacen hotuna masu motsi, da sauran lamurori.
 2. A cusawa musulmai kaunar yiwa daulolinsu bore, a kuma baiwa duk wata kungiya mai rajin yin haka tallafi.
 3. A karya kashin bayan tattalin arzikin musulmai. A kaskantar da dukkan hanyoyin su na kuɗin shiga, a cusa musu rashin son yin salloli, a kuma yawaita giya da kayyakin maye a cikinsu.

 

Nayi zama na tsawon wata ɗaya a landan bayan na kammala jin waɗannan sirrika, sannan aka aike mini cewar lokacin sake fita ta yayi, kuma a wannan karon so ake naje na kara haɗuwa da muhammad Najd.

A lokacin da zan tafi ne Sakataren mu ke faɗa mini cewar akwai bukatar a wannan karon kada nayi kasala akan Muhammad Najd, domin har zuwa yanzu ‘yan leken asirin su sun sanar musu da cewar bai riga ya gane tarkon da yake shirin faɗawa ba.

Sakataren yace mini “wakilin mu yayi magana dashi a Isfahan, ya kuma aminta da yarje-jeniyar da suka kulla akan cewar akwai aiyukan da zaiyi, mukuma zamu bashi tsaro da dukkan taimakon dayake da bukata”.

Na samu cikakken farin cikin jin haka, sannan na tambayi Sakataren mu abinda ya kamata nayi idan mun haɗu dashi.

Sai yace mini “Hukumar mu ta sanya ka’i’doji da take son Muhammad Najd Zai cimma kamar haka:-

 1. Zaiyi ikirarin cewar duk wani musulmi kafiri ne, kuma zaice kisansa ya halatta, matansa kuma sun cancanci zamowa bayi a siyar dasu a kasuwa matsawar wannan musulmin baibi turbar da yazo da ita ba.
 2. Zaiyi ikirarin cewar ɗakin Ka’aba gunki ne don haka dole a rushe shi a daina yi masa bauta.
 3. Zai hana musulmi yin biyayya ga halifofi, zai kuma haɗa runduna domin samun iko dasu.
 4. Zai yi ikirarin hana duk wani wajen da musulmai ke zuwa ziyara a matsayin wurin bautar gumaka, don haka zai hana yin ziyara a wuraren. Zai kuma samar da kafar zagin Annabi da sahabbansa.
 5. Zaiyi kokarin samar da sabon littafin fassarar Alkurani maigirma mai ɗauke da gurɓatacciyar fassara da ragin ayoyi”.

Sannan sakataren yace mini “waɗannan sune abubuwan da akeso na tsaya kai da fata don ganin Muhammad ya cimma, amma hukumar mu ba gaggawa take ba, don haka bata damu da tsawon lokacin da tabbatuwar muradun zai ɗauka ba”.

Bana mantawa lokacin da zan fita daga gidana zuwa Basra, yaro na Rasputin yana ɗaga mini hannu yana cewa “kadawo da wuri Baba”. Nan take naji idanuwa na sun cika da kwalla har saida na kasa ɓoye damuwata ga mai ɗaki na.

 

Za mu cigaba a makon gobe in sha Allah.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!