Connect with us

BIDIYO

Masu Wasan Barkwanci Sun Nemi Gwamnati Ta Taimaka Musu

Published

on

Wadansu ba’adin masu wasan Barkwanci sun nemi gwamnati da ta tallafa musu domin bunkasa harkokin kasuwancinsu da kuma rage zaman rashin aikin yi a kasa a tsakanin al’umma.

Sun bayyana hakan ne a lokacin da suke nazarin irin gudummawar da suke baiwa tattalin arzikin Nijeriya a shekarar 2018. Sun bayyanawa kamfanin dillancin Nijeriya cewa; kamfaninsu da suke wasannin barkwanci yana da matukar tasiri wajen jawo hankalin matasa wadanda ba su samun aikin yi.

Sun tabbatar da cewa; da a ce gwamnatin na tallafawa musu da kudi, to da zai rage rashin aikin yi a kasarnan, da kuma rage radadin damuwa a cikin al’ummarnan. Sun bayyana cewa; idan aka ragewa mutane damuwa, rayuwar al’umma za su dade.

Akinlade Richard, wanda aka fi sani da  MC Richard, ya ce; shekaarr 2018 shekara ce da suka sha wahala, domin mafi yawan kamfanoni ba su yi tarukan karshen shekara ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!